Lauya ya ce sai Ibrahim Magu ya kare kansa a gaban kwamiti kafin a fitar da rahoto
Wani lauya da ya tsayawa tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya yi tir da rahoton da ke yawo na cewa kwamiti ya bada shawara a tsige Magu.
Bayan kira ga shugaban kasa da ake rade-radin wannan kwamitin bincike ya yi, ana jita-jitar cewa an bukaci Muhammadu Buhari ya maka Magu a gaban kotu.
Tsohon shugaban na hukumar EFCC ta bakin lauyansa, Wahab Shittu, ya ce har yanzu bai gabatar da hujjojin da ke kare wanda kwamitin ya ke bincike ba.
Lauyan ya ke cewa daga yau ne Magu zai fara kare kansa. Kwamitin binciken shugaban kasa da ke karkashin Ayo Salami zai saurari hujjoji da shaidunsa.
“Ku sani cewa an kawowa kwamitin bincike makamancin irin rahoton da aka fitar a wata jarida, kuma shugaban kwamitin ya bamu shawarar mu yi watsi da labarin.”
Lauyan ya kara da cewa: “Halinmu shi ne mu yi fatali da wannan sabon rahoto a matsayinsa na labarin karya, wanda ba ya nuna ainihin halin da ake ciki.”
KU KARANTA: Za a kai Soja gaban Alkali saboda sukar Janar Buratai
A cewar Shittu, sai da aka shafe kwanaki 35 ana wannan bincike, ba a ji ta bakin Magu ba. Kwamitin binciken ya nemi jin ta bakin Magu ne a farkon Agusta.
Bayan sauraron hujjojin da Magu zai bada domin ya wanke kansa, kwamitin bai kai ga jin ta bakin Ministan shari’a ba, wanda wasikarsa ta jawo aka fara binciken EFCC.
Ya ce: “Da farko an hana wanda mu ke karewa hallarar zaman kwamiti, inda shaidu da-dama su ka rika bada shaida ba tare da ya samu damar yi masu tambayoyi ba.”
Shittu ya ce sai yanzu ne tsohon shugaban na EFCC ya samu damar zama a gaban kwamitin. Hana Magu takardun binciken ya sa lauyoyinsa su ka kai kara a kotu.
Babban Lauyan ya ke cewa abin ban tsoro ne aji cewa kwamitin Ayo Salami ya kai wa shugaban kasa rahoton farko kafin ya kai ga sauraron abin da Magu zai fada.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng