Mun kama mutum 47 bayan ‘Yan IPOB sun kashe mana Jami’ai 2 – Hukumar DSS

Mun kama mutum 47 bayan ‘Yan IPOB sun kashe mana Jami’ai 2 – Hukumar DSS

Akalla mutum biyu aka rasa a cikin dakarun hukumar DSS masu fararen kaya, bayan rikici ya barke tsakanin jami’an tsaron da ‘yan kungiyar IPOB.

‘Yan tawayen sun bayyana cewa su ma sun rasa mutane 21, bayan haka jami’an tsaron sun kama yara 47 daga cikin ‘yan kungiyar IPOB masu fafukar Biyafara

Premium Times ta ce wannan lamari ya jawowa mutane zaman dar-dar bayan an aika sojoji da ‘yan sanda zuwa yankin da wannan mummunar rigima ta kaure.

Wasu wadanda rikicin ya faru a gaban idanunsu, sun shaidawa ‘yan jarida cewa jami’an tsaro sun rika bi lungu-lungu su na laluben ‘ya ‘yan kungiyar IPOB.

Mai magana da yawun bakin hukumar DSS na kasa, Mista Peter Afunanya ya shaida cewa an kai wa dakarunsu hari ne a garin Emene da ke jihar Enugu.

Peter Afunanya ya daurawa kungiyar IPOB alhakin kai masu harin da ya yi sanadiyyar rasa ma’aikata biyu na hukumar. Afunaya ya ce haka kawai aka takalesu.

KU KARANTA: A tashi tsaye a kan cin kashin da ake yi wa Musulmai a Sin - Ba

Mun kama mutum 47 bayan ‘Yan IPOB sun kashe mana Jami’ai 2 – Hukumar DSS
Wasu 'Yan kungiyar IPOB
Asali: UGC

“Hukuma ta rasa jami’ai biyu a harin da kungiyar IPOB ta kawo mana karara babu gaira babu dalili.” Inji Afunanya a jawabin da ya fitar a madadin DSS.

Mista Afunanya ya kara da cewa: "Hukuma ta na yi wa iyalin wadannan jami‘ai da aka rasa ta’aziyya, tare da addu’ar Ubangiji ya jikansu.”

“Sai dai an dauki duk matakai na ganin an cafke masu hannu a wannan danyen aiki, da nufin a hukuntasu. Bayan haka za a gudanar da cikakken bincike.”

“Har ila yau, hukumar ta na kara jaddada kokarinta na aiki da sauran jami’an tsaro wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.” Inji kakakin na DSS.

Afunanya ya yi kira a madadin DSS ga jama’a su zama masu bin doka, ya kuma nemi mutane su cigaba da harkokin gabansu ba tare da jin tsoron komai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng