Sokoto: Yadda 'yan bindiga suka sace amarya da mai jego
Wasu jama'a da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da sabuwar amarya tare da wata mai jego a kauyen Sutti da ke karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.
Wata majiya ta ce, an sace amaryar ne yayin da jerin tawagar motoci ke kai ta gidan mijinta a ranar Laraba, 19 ga watan Augusta.
Kamar yadda majiyar ta ce, mai jegon ita ce matar Magajin Garin Sutti kuma har gida aka bi ta aka saceta da jinjirinta a daren Alhamis.
Majiyar ta sanar da Daily Trust cewa, har yanzu ba a san yawan jama'ar da 'yan bindigar suka sace ba a kan babbar hanyar Balle zuwa Tangaza a ranar Laraba.
"'Yan kasuwar na dawowa daga Tangaza inda suka nufa Balle a motocin haya biyu. Sun fada kan shingen kan titi wanda 'yan bindigar suka saka, a take kuma suka umarcesu da su fito daga cikin ababen hawan sannan suka yi awon gaba da su.
"Har zuwa ranar Juma'a da ta gabata, ba a ji komai game da su ba kuma ababen hawansu na nan wurin inda aka iza keyarsu," majiyar ta kara da cewa.
KU KARANTA: Dumu-dumu: Yadda aka kama matasa biyu suna luwadi da junansu
Majiyar ta kara da cewa, 'yan bindigar sun harba daya daga cikin direbobin, amma an sallamo shi daga asibiti. Sauran ba su tashi daga jinyar ba duk sun mutu.
Daily Trust ta gano cewa, wasu daga cikin kauyawan sun kauracewa kauyukansu sakamakon tsoron hare-haren da suke.
"Akwai wani kauye mai suna Garin Alfarma wanda da yawa daga cikin mazaunansa suka koma Gidan Madi, babbar birnin karamar hukumar Tangaza, saboda tsoron 'yan bindigar," yace.
Wata majiya daga jami'an tsaro ta sanar da Daily Trust cewa, masu garkuwa da mutane sun saka kananan hukumomin Gudu da Tangaza a gaba, ballantana da dare.
"Sau da yawa 'yan bindigar na aiwatar da miyagun ayyukansu ne da dare. Suna zuwa kauyukan da jami'an tsaro basu iya zuwa da wuri sannan su sace jama'a," yace.
"A ranar Asabar da ta gabata, mun damke wasu wadanda ake zargin 'yan bindiga ne tare da masu kai musu bayanai a karamar hukumar Gudu," yace.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, ASP Muhammad Sadiq, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an hada sintirin hadin guiwa don kula da yankin.
"Mun tsananta sintiri don bada kariya ga yankin, ceto wadanda aka sace da kuma damke 'yan ta'addan," yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng