Dubban masoya sun yi tururuwar fitowa a Kaduna domin tarban tsohon Sarkin Kano, Sanusi

Dubban masoya sun yi tururuwar fitowa a Kaduna domin tarban tsohon Sarkin Kano, Sanusi

- Masoya sun yi tururuwar fitowa manyan hanyoyi a Kaduna domin yi wa tsigaggen Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi maraba da zuwa jihar

- Babu masaka tsinke a manyan hanyoyi da suka hada da Kawo, Ali Akilu road da Ahmadu Bello Way yayinda motoci, babura da adaidaita sahu suka mara masa baya

- Sanusi ya je Kaduna ne domin ganawa da magoya bayansa, wanda wasun su sun fito ne daga jihar Kano kuma zai gana da tsohon amininsa

Dubban masoya a ranar Lahadi, 23 ga watan Agusta, sun fito manyan hanyoyi a Kaduna domin yi wa tsigaggen Sarkin Kano kuma tsohon shugaban babban bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi maraba da zuwa jihar Kaduna.

An samu cinkoson jama’a a manyan hanyoyi da suka hada da Kawo, Ali Akilu road da Ahmadu Bello Way yayinda motoci, babura da adaidaita sahu suka dunga rera wakar yabon Sanusi tare da yi wa motarsa rakiya a kewayen birnin Kaduna.

Wani jirgi mai zaman kansa ya isa hedkwatar horar da rundunar sama a Kaduna da misalin karfe 10:30 na yau Lahadi.

‘Yan jarida tare da wasu masu sarauta daga jihar Kano sun taru a hedkwatar rundunar sojin saman da misalign karfe 9:30 na safe amma aka hana su shiga sansanin.

Dubban masoya sun yi tururuwar fitowa a Kaduna domin tarban tsohon Sarkin Kano, Sanusi
Dubban masoya sun yi tururuwar fitowa a Kaduna domin tarban tsohon Sarkin Kano, Sanusi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya samu rakiyar matansa da sauran hadimai, sannan ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati a jihar kafin tawagarsa suka garzaya zuwa gidan gwamnatin jihar.

Sanusi ya je Kaduna ne domin ganawa da magoya bayansa, wanda wasun su sun fito ne daga jihar Kano kuma zai gana da tsohon amininsa kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Daga cikin wadanda suka je tarban Sarkin, harda fitaccen mawakin Kannywood kuma sarkin wakarsa, Nazir Ahmad wanda aka fi sani da sarkin wakar san Kano.

An nada Sanusi a matsayin sarkin Kano na 14 a ranar 8 ga watan Yunin 2014, biyo bayan mutuwar Sarki Ado Bayero.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwararren makashi Shodipe ya sake shiga hannu bayan saka kyautar kudi ga wanda ya fallasa shi

Amma sai Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, a ranar 9 ga watan Maris, 2020, ya tsige shi kan zargin nuna rashin biyayya ga hukumomi.

Daga nan sai aka dauke Sanusi zuwa Loko a jihar Nasarawa kafin daga nan aka mayar da shi Awe duk a jihar inda ya yi kwanaki uku kafin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi umurnin sakinsa daga inda aka tsare shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel