Taron NBA: A janye gayyatar da aka yi wa Obasanjo da Wike suma – Kungiyar lauyoyi Musulmai

Taron NBA: A janye gayyatar da aka yi wa Obasanjo da Wike suma – Kungiyar lauyoyi Musulmai

Kungiyar lauyoyi Musulmai na Najeriya ta bukaci kungiyar NBA da ta janye gayyatar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Ta nemi a cire sunayen shugabannin biyu cikin masu jawabi a babban taronta da za a yi a ranar 26 zuwa 29 ga watan Agusta.

Hakan na zuwa ne bayan shugabannin kungiyar sun yanke shawarar janye gayyatar da suka yiwa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai sakamakon zanga-zangar da wasu lauyoyi suka yi a kan haka.

Lauyoyin sun yi korafin cewa an sha zargin Gwamna El-Rufai da take hakkin bil adama.

Shugabannin NBA sun amsa koken lauyoyin sannan suka janye gayyatar da suka yi wa gwamnan.

Hakan ya janyo cece-kuce. Mambobin kungiyar reshen jihohin Jigawa da Bauchi sun yi barazanar kauracewa taron idan har ba a janye lamarin ba.

A wata hira da jaridar Punch a ranar Asabar, shugaban kungiyar lauyoyin Musulmai, Ibrahim Abikan, ya ce kungiyarsa na adawa da kasancewar Obasanjo da Wike a wajen taron saboda an kama su suma da irin laifin da ake zargin Gwamna El-Rufai da shi.

Taron NBA: A janye gayyatar da aka yi wa Obasanjo da Wike suma – Kungiyar lauyoyi Musulmai
Taron NBA: A janye gayyatar da aka yi wa Obasanjo da Wike suma – Kungiyar lauyoyi Musulmai Hoto: Pointblank
Asali: UGC

“Mun dage cewa idan har akwai wani mataki da aka bi wajen janye gayyatar El-Rufai, to a bi wannan mataki a kan sauran masu jawabi a taron.

"El-Rufai ya kasance jami’in gwamnati kuma ya zama dole a janye gayyatar duk wanda ake zargi da take hakkin bil adama cikin sauran mutanen da aka gayyata. Muna so a yi amfani da wannan mataki kan Obasanjo da Wike."

KU KARANTA KUMA: An kama wani matashi bayan ya saci dan kamfai na mata da aka yi amfani da su har guda 14

Mutane sun fara aiko min da korafe-korafe a kan zargin take hakkin bil adama da rashin mutumta doka na Obasanjo da Wike.

Sun fara tura shi ga kwamitin shirya taron NBA da ita kanta NBA.

“Matsayarmu shine cewa duk wanda zai yi jawabi a wajen ya iya gabatar mana da jawabai masu inganci.” In ji Abikan.

Haka, tsohon shugaban kungiyar MULAN, Funminiyi Adeleke, a wata hira daban, ya yi watsi da hukunccin shugabannin kungiyar NBA na janye gayyatar da suka yiwa El-Rufai.

Ya yi korafin cewa Obasanjo da Wike ma basu cancanci jawabi a taron ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel