An kama wani matashi bayan ya saci dan kamfai na mata da aka yi amfani da su har guda 14

An kama wani matashi bayan ya saci dan kamfai na mata da aka yi amfani da su har guda 14

- Wani matashi mai suna Adeniyi Muhammed ya shiga hannun 'yan sanda a kan satar dan kamfai na mata da aka yi amfani dasu guda 14 a jihar Ogun

- An kama wanda ake zargin ne bayan wata mazauniyar unguwar Kano a yankin Ayetoro da ke jihar ya shigar da kara a kan satar dan kamfenta a ranar Talata, 18 ga watan Agusta

- Sai dai ya ce wani ne ya aike shi sato dan kamfen, kuma ana kokarin ganin an kamo shi

An kama wani matashi mai suna Adeniyi Muhammed dan shekaru 16 dauke da dan kamfai na mata da aka yi amfani dasu guda 14 a jihar Ogun, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kakakin ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan wata mazauniyar unguwar Kano a yankin Ayetoro da ke jihar ta shigar da kara a kan satar dan kamfenta a ranar Talata, 18 ga watan Agusta.

An kama wani matashi bayan ya saci dan kamfai na mata da aka yi amfani da su har guda 14
An kama wani matashi bayan ya saci dan kamfai na mata da aka yi amfani da su har guda 14 Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Oyeyemi ya ce: “An gudanar da bincike a gidan da yake zaune sannan aka samo wasu karin ‘yan kamfai 14. Wanda ake zargin ya tona cewar ya aikata laifin amma ya yi ikirarin cewa wani ne ya tura shi domin ya samo masa ‘yan kamfen. Ana kokarin ganin an kamo abokin aikin nasa.”

KU KARANTA KUMA: 'Yan gudun hijira na shiga kungiyar Boko Haram - Gwamna Zulum ya koka

An kuma tattaro cewa kwamishinan yan sandan jihar, Edward Ajogun ya yi umurnin cewa a tura wanda ake zargin zuwa sashin binciken laifuffuka na jihar domin ci gaba da bincike.

A wani labarin, an yanke wa wani matashi dan shekaru 19 mai suna Olasunkanmi Yekini hukuncin dauri har na tsawon shekaru shida a kurkuku akan laifin satar wayar N6,000.

An kuma kama shi da laifin satar dan kamfai na mata guda uku wanda yayi sanadiyar rufe shi.

Dan sanda mai gabatar da kara, Jefani Musilimi ya fada wa kotu cewa Olasunkanmi ya aikata laifin a ranar 28 ga watan Janairu a Ibokun road, yankin Oja-Oba, Osogbo.

Jefani yace Olasunkanmi ya shiga dakin wata matashiya mai suna Folashade Ganiyu inda ya sace dan kamfai uku a dakin wankanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel