Hausawa 'yan biyu, suka auri 'yan biyu, kuma duka suka haifi 'yan biyu

Hausawa 'yan biyu, suka auri 'yan biyu, kuma duka suka haifi 'yan biyu

Saidu Yusuf da Sa'adu Yusuf yan biyu ne kuma yan asalin jihar Jigawa masu labarin ban mamaki.

Sun auri mata yan biyu, Hassana Iliyasu da Hussaina Ilyasu; daga garin Daura, jihar Katsina kuma suka haifawa kowanne cikinsu yan biyu.

Yayinda sukayi hira da jaridar Punch, Saidu ya ce ya auri Hassana, yayinda dan uwansa Sa'adu ya auri Hussaina.

Yace: "Mun yan biyu ne kuma muka auri yan biyu. A al'ada da addini, mun halarci mabanbantan makarantun Islamiyya."

Hakazalika mun halarci makarantar firamaren Nuruddeen dake Jenta, Jos, jihar Plateau; makarantan gwamnatin Birnin Kudu, jihar Jigawa; makarantar koyon ilmin kiwon laifya, Jahun, jihar Jigawa inda muka difloma, sannan jami'ar Maryam Abacha dake Nijar, inda mukayi digiri a MLT."

"Mu yan jihar Jigawa ne amma a Jos muka girma."

Shi kuma Sa'adu ya bayyana cewa: "Tun farko muna da niyyar auren yan biyu. Amma mun san Allah ne kadai zai iya wanzar da haka. Mun yi soyayya da mata da ba yan biyu ba amma muka auri yan biyu cikin ikon Allah."

"A Junairun 2014 wani mutum mai suna Mallam Zakariya ya hada mu da yan biyun da muka aura. Yan jihar Katsina ne, Daura."

"Daga baya muka hadu da su kuma mukayi aure ranar 30 ga Agusta, 2014. Rana daya mukayi aure kuma abin tarihi ne garemu."

Saidu yace a matsayinsu na yan biyu, sun yi matukar farin cikin haifan yan biyu.

Sa'adu ya ce matarsa ta haifi mata yan biyu, Nasibah da Nusaibah ranar 15 ga Yuni, 2015 yayinda Saidu ya ce matarsa ta haifi yan biyu maza Sahl da Suhail, ranar 17 ga Yuni, 2015.

Hausawa 'yan biyu, suka auri 'yan biyu, kuma duka suka haifi 'yan biyu
Hausawa 'yan biyu, suka auri 'yan biyu, kuma duka suka haifi 'yan biyu
Asali: Twitter

Matar Saidu, Hassana, ya ce ita da yar'uwarta sun halarci GGSS Rogogo a jihar Kastian da Yusuf Bala Usman College of Legal and General Studies, Daura, inda suka karancin Hausa da ilimin addinin Musulunci.

Tace: "Muna matukar farin ciki da alfahari auren yan biyu irinmu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel