Ni dan a mutun Aisha Muhammadu Buhari ne - Fani Kayode

Ni dan a mutun Aisha Muhammadu Buhari ne - Fani Kayode

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa shi dan a mutun uwargidar shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ne saboda ita ce hasken fadar shugaban kasa.

Fani-Kayode, a wasu jerin wallafa da ya yi a shafin Twitter, ya yi wa Aisha Buhari maraba da dawowa gida daga Dubai inda ta je jinya.

Ya ce babu mai dakatar da uwargidar shugaban kasar domin Allah zai ci gaba da kasancewa tare da ita, inda ya yi mata addu’an samun karfi.

Fani-Kayode ya kara da cewar wadanda suke ganin jinjinawar da ya yiwa Aisha Buhari na nufin yana shirin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), toh su sauya tunani domin har abada hakan ba mai kasancewa bane.

Ni dan a mutun Aisha Muhammadu Buhari ne - Fani Kayode
Ni dan a mutun Aisha Muhammadu Buhari ne - Fani Kayode
Asali: UGC

“Barka da dawowa gida ya uwargidar shugaban kasarmu, Aisha Buhari. Na sake maimaitawa, ke ce hasken Villa. Babu abunda zai dakatar da ke kuma Allah na tare da ke. Ke tsaya da karfinki.

“Ga wadanda suke ganin cewa hakan na nufin zan koma APC, na fada ku farka sannan ku daina daukar mafarkinku a matsayin gaskiya. Baya nufin haka ko kadan.

KU KARANTA KUMA: Rundunar 'yan sanda ta sa kyautar N500K ga wanda ya tona mabuyar kwararren makashi Shodipe

Uwargidar shugaban kasarmu ta dawo gida cikin koshin lafiya bayan zuwa Dubai shine wasu ke cewa kada mu yi mata fatan alkhairi sannan mu yi godiya ga Allah da ya tsare rayuwarta ya kuma dawo mana da ita gida lafiya kawai saboda muna ‘yan adawa? Wasu mutanen basu da tausayi kuma mugwaye ne! Allah ya taimake mu,” in ji shi.

A baya mun ji cewa an garzaya da uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, birnin Dubai, kasar UAE don jinyan ciwon wuyan da take fama da shi tun bayan zuwanta Legas, Daily Trust ta ruwaito.

An samu labarin cewa uwargidan shugaba Buhari ta tafi Dubai ne tun washe garin Sallah sakamakon ciwon wuya da take fama dashi bayan komawa birnin tarayya Abuja daga jihar Legas.

Za ku tuna cewa a watan Yuli, Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya ga Mrs Florence Ajimobi, uwargidan tsohon gwamnan Oyo, Abiloa Ajimobi, a gidansu dake Glover Road, Ikoyi, jihar Legas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng