Daga ‘Dan autansu zuwa babban cikinsu, Ministocin Gwamnatin Tarayya

Daga ‘Dan autansu zuwa babban cikinsu, Ministocin Gwamnatin Tarayya

Mun kawo maku cikakken bayani game da Ministocin tarayyar Najeriya. Legit.ng Hausa ta jero Ministocin ne bisa yawan shekarun da su ka yi a Duniya.

A wannan jeri za ku fahimci cewa, Sadiya Umar Faruk, Isa Ali Ibrahim Pantami, Ramatu Tijjani da Festus Keyamo ne kawai ba su haura shekaru 50 da haihuwa ba.

Akwai akalla Ministoci biyar da sun ba shekaru 70 baya; daga cikinsu akwai ministan lafiya, ministan harkar gona, ministan tsaro da shi kan sa shugaban kasa.

Ga yadda jerin ya ke kamar yadda Stati Sense su ka yi bincike kwanaki:

1. Sadiya Umar Faruk [shekara 45] – Ministar bada agaji da walwala

2. Isa Ali Ibrahim Pantami [shekara 47] – Ministan sadarwa

3. Festus Keyamo [shekara 50] – Karamin Ministan kwadago

4. Ramatu Tijjani [shekara 50] – Karamar Ministar Abuja

5. Uche Ogah [shekara 51] – Karamin Ministan ma’adanai

6. Hon. Emeka Nwajiuba [shekara 52] – Karamin Ministan ilmi

7. Mohammed Abdullahi [shekara 52] – Karamin Ministan kimiyya da fasaha

8. Zubairu Dada [shekara 52] – Karamin Ministan harkokin kasar waje

9. Abubakar Malami SAN [shekara 53] – Ministan shari’a, AGF

10. Sunday Dare [shekara 54] – Ministar matasa da wasanni

11. Abubakar Aliyu [shekara 54] – Karamin Ministan gidaje da ayyuka

12. Gbemisola Saraki [shekara 55] – Karamar Ministar sufuri

13. Rotimi Amaechi [shekara 56] – Ministan sufuri

14. Timipre Sylva [shekara 56] – Karamin Ministan fetur

15. Hadi Sirika [shekara 56] – Ministan harkokin jiragen sama

16. Babatunde R. Fashola [shekara 56] – Ministan gidaje da ayyuka

17. Clement Ike [shekara 56] – Karamin Ministan kasafin kudi

18. Godswill Akpabio [shekara 57] – Ministan Neja-Delta

19. Sulaiman Adamu [shekara 57] – Ministan ruwa

20. Sharon Ikeazor [shekara 58] – Karamar Ministar muhalli

21. Olamilekan Adegbite [shekara 58] – Ministan ma’adanai

KU KARANTA: Ministan kasar wajen Najeriya ya sokii juyin mulkin da aka yi a Mali

Daga ‘Dan autansu zuwa babban cikinsu, Ministocin Gwamnatin Tarayya
Taron Ministocin Gwamnatin Tarayya
Asali: UGC

22. Mustapha Shehuri [shekara 59] – Karamin Ministan gona

23. Zainab Ahmed [shekara 60] – Ministar kudi

24. Mohammed Musa Bello [shekara 61] – Ministan Abuja

25. Goddy Jedy Agba [shekara 61] – Karamin Ministan wuta

26. Paul Tallen [shekara 61] – Ministar mata

27. Adeniyi Adebayo [shekara 62] – Ministan kasuwanci

28. Saleh Mamman [shekara 62] – Ministan wuta

29. Mohammed Mahmod [shekara 63] – Ministan muhalli

30. Rauf Aregbesola [shekara 63] – Ministan cikin gida

31. Adamu Adamu [shekara 64] – Ministan ilmi

32. Geoffrey Onyeama [shekara 64] – Ministan kasar waje

33. Maryam Katagum [shekara 65] – Karamar Ministar kasuwanci

34. George Akume [shekara 65] – Ministan harkokin musamman

35. Adeleke Mamora [shekara 67] – Karamin Ministan kiwon lafya

36. Maigari Dingyadi [shekara 67] – Ministan ‘yan sanda

37. Chris Ngige [shekara 68] – Ministan kwadago

38. Ogbonnaya Onu [shekara 68] – Ministan kimiyya da fasaha

39. Lai Mohammed [shekara 68] – Ministan sadarwa da al’adu

Wadannan su ne rukunin wadanda su ka fi shekaru:

40. Bashir Magashi [shekara 71] – Ministan tsaro

41. Tayo Alasoadura [shekara 71] – Karamin Ministan Neja-Delta

42. Osagie Ehanire [shekara 73] – Ministan kiwon lafiya

43. Sabo Nanono [shekara 74] – Ministan noma

44. Muhammadu Buhari [shekara 77] – Ministan man fetur

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel