Annobar korona: Jerin jihohi 16 da suka samu tallafin N1.6bn daga bankin duniya

Annobar korona: Jerin jihohi 16 da suka samu tallafin N1.6bn daga bankin duniya

Kwamitin raya tattalin arzikin kasa (NEC) ya ce jihohi 16 sun karbi tallafin miliyan N100 daga bankin duniya domin samun saukin matsin tattalin arziki da aka shiga sakamakon dokar kulle saboda annobar korona.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ne ya sanar da hakan yayin tattaunawarsa ta yanar gizo da manema labarai bayan kammala taron NEC ta mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo, ya jagoranta ranar Alhamis.

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne bankin duniya ya yi tayin bawa jihohi tallafin jimillar dalar Amurka $1.5bn domin rage radadin matsin tattalin arziki da aka shiga saboda annobar korona.

Jihohin 16 da gwamna Sule ya bayyana cewa sun karbi tallafin sune kamar haka; Ekiti, Gombe, Niger, Sokoto, Taraba, Oyo, Abia, Enugu, Zamfara, Bauchi, Ebonyi, Kaduna, Kwara, Cross River, Imo, da Delta.

"Sauran jihohi biyar da yanzu ke kan layi jiran samu nasu kason sune; Filato, Yobe, Ondo, Benue da Osun yayin da har yanxu ake jiran bayanan asusun jihar Nasarawa," a cewar gwamna Sule.

Gwamnan ya bayyana cewa sun tattauna batun matakan da aka dauka yayin kara tsawon wa'adin sassauta dokar kulle a zagaye na biyu.

Kazalika, ya kara da cewa NEC ta karbi sabon rahoto daga kwamitin wucin gadi da ta kafa a kan tsaro da harkar 'yan sanda.

Annobar korona: Jerin jihohi 16 da suka samu tallafin N1.6bn daga bankin duniya
Abdullahi Sule; gwamnan jihar Nasarwa
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa NEC ta yi doguwar muhawara a kan matsalar tabarbarewar tsaro a sassan kasa, musamman kalubalen kungiyar Boko Haram da har yanzu ake fama da shi a yankin arewa maso gabas.

DUBA WANNAN: NBA ta janye gayyatar El-Rufa'i zuwa babban taronta na kasa, ta bayyana dalili

"Bayan tattaunawarmu a kan matsalar tsaro a ranar 20 ga watan Yuni, an kafa kwamitin wucin gadi da zai duba halin da tsaron kasa ke ciki da kuma irin kalubalen da tsaro ke fuskanta.

"Gwamnan jihar Ekiti ne ya shugabanci kwamitin wucin gadin, wanda ya fara gudanar da zamansa a ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta," a cewar gwamna Sule.

Gwamnan ya bayyanna cewa kwamitin ya tattauna tare da samun rahotanni daga ofishin mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro (NSA), ofishin babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), rundunar soji da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel