Jam’iyyar PDP ta yi babban kamu a Abuja, mambobin APC sama da 200 sun dawo cikinta

Jam’iyyar PDP ta yi babban kamu a Abuja, mambobin APC sama da 200 sun dawo cikinta

- 'Ya'yan jam'iyyar APC sama da guda dari biyu sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, a ranar Laraba, 19 ga watan Agusta, a yankin Kuje da ke babbar birnin tarayya, Abuja

- Masu sauya shekar sun samu tarba daga Alhaji Mohammed Ismaila, Shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Kuje

- Shugaban masu sauya shekar, Mohammed Gambo ya bayyana cewa basu gamsu da tsarin manuofin APC ba

Mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sama da guda dari biyu sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Democratic Party (PDP), a ranar Laraba, 19 ga watan Agusta, a yankin Kuje da ke babbar birnin tarayya, Abuja.

Masu sauya shekar sun samu tarba daga Alhaji Mohammed Ismaila, Shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Kuje, a gidan gwamnatin karamar hukumar.

Sun mika katunan shaidar kasancewarsu mambobin APC, tsinstiya da fastocinsu domin a musanya masu da na PDP.

Jam’iyyar PDP ta yi babban kamu a Abuja, mambobin APC sama da 200 sun dawo cikinta
Jam’iyyar PDP ta yi babban kamu a Abuja, mambobin APC sama da 200 sun dawo cikinta Hoto: The Sun
Asali: UGC

Mohammed Gambo, Shugaban masu sauya shekar, a cikin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya bayyana cewa bai gamsu da tsarin manufofin APC ba.

Ya bayyana cewa sun yanke shawarar komawa PDP ne domin bayar da gudunmawa ga ci gaban karamar hukumar Kuje.

“Mun sauya sheka zuwa PDP domin ci gaban Kuje da Najeriya baki daya.

“Zamanmu a APC bai da wani tasiri. Manufofin APC da tsarin bai karfafa damokradiyya da shugabanci a yankin ba,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Rayuwa bata taba wuya irin haka ba – Audu Ogbeh ya bukaci FG ta dakatar da kashe-kashe

Da yake tarban masu sauya shekar, Shugaban PDP a yankin Kuje ya ce akwai karin masu sauya sheka da za su dawo jam’iyyar domin ci gabanta da na Kuje.

Ismaila ya bayyana cewa PDP za ta lashe mukamin shugabanci a yankin Kuje domin ci gaban yankin da kasar.

A wani labarin kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya nuna babu abin da ya hada shi da hotunansa da ake gani su na zagaye gari da nufin zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Dr. Kayode Fayemi ya ce babu ruwansa da wadannan fostoci da wani shugaban karamar hukuma na jihar Ekiti ya fito da su a kafafen yada labarai da sadarwa na zamani.

Mai girma gwamnan ya ce Femi Ayodele bai da hurumin da zai fito da fosta da sunan zai yi takara a zaben 2023. Ayodele shi ne shugaban karamar hukumar Ikere a Ekiti.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel