Ba a ga watan sabuwar shekarar Musulunci ba, gobe Juma’a ne 1 ga watan Muharram

Ba a ga watan sabuwar shekarar Musulunci ba, gobe Juma’a ne 1 ga watan Muharram

Kwamitin duban wata ta kasa karkashin majalisar koli ta harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya bayyana cewa babu rahoton ganin sabon jinjirin watan Muharram 1442.

Hakan na nufin cewa ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta zai kasance Dhul-Hijja 1441, yayinda Juma’a zai zama 1 ga watan Muharram, sabuwar shekarar Musulunci ta 1442.

“Zuwa karfe 7:38 na dare babu rahoton ganin sabon wata a Najeriya, saboda haka mai alfarma Sarkin Musulmi bai bayyana Alhamis a matsayin 1 ga watan Muharram 1442 ba.

“Don hakan gobe (Alhamis) ita ce 30 ga watan Dhul Hijja 1441, sannan Juma’a za ta zama 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar Musulunci," wani mamba na kwamitin NMSC, Sheikh Salihu Muhammad Yakub ya bayyana.

Ba a ga watan sabuwar shekarar Musulunci ba, gobe Juma’a ne 1 ga watan Muharram
Ba a ga watan sabuwar shekarar Musulunci ba, gobe Juma’a ne 1 ga watan Muharram
Asali: UGC

Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin bayar da shawarwari a kan harkokin addini na majalisar Sultan, Sokoto, ya fitar da wata sanarwa.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin ya bayyana cewa Laraba, 19 ga watan Agusta, 2020, daidai yake da 29 ga Dhul-hijja 1441, kuma a ranar ne za a fara neman sabon jinjirin watan Muharram 1442.

KU KARANTA KUMA: Zamu sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda ya zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya

Sanarwar ta bukaci Musulmi da su kai “rahoton ganin watan ga sarakunan yankunansu domin su nasar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar”, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan za ku tuna mun kawo maku cewa Gwamnatin jihar Kano ta bada hutun aiki a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta, domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci.

Sanarwar hakan ta fito ne cikin wani sako da hadimin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan sabuwar hanyar sadarwa ta zamani, Salihu Tanko Yakasai ya wallafa a Twitter.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar Musulmin jihar da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya da karuwar arziki.

Ganduje ya kuma yi addu’a kan Allah ya kawo wa jihar dauki daga annobar korona da kuma matsin da mutane suke ciki.

Ganduje ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da bunkasa rayuwar al’ummar jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel