Mai Rahamaniyya Oil and Gas Limited zai yi zaman kaso a Birtaniya

Mai Rahamaniyya Oil and Gas Limited zai yi zaman kaso a Birtaniya

- Wata Kotu da ke Ingila ta samu kamfanin Rahamaniyya Oil and Gas da aikata laifi

- A dalilin haka an yankewa shugaban Rahamaniyya hukuncin zama a gidan yari

- Abdulrahman Bashir zai shafe watanni goma ya na tsare a gidan kaso a Birtaniya

Babban ‘dan kasuwan Arewacin Najeriya wanda ya yi fice a harkar mai, Alhaji Abdulrahman Bashir, ya samu kan shi a matsala da hukumomin kasar Ingila.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto na musamman a ranar 19 ga watan Agusta, 2020, ta ce an yankewa shugaban kamfanin Rahamaniyya Oil & Gas hukuncin dauri.

A watan Fubrairu, wata kotu mai iko da kasashen Ingila da Wales ta zartarwa Abdulrahman Bashir da waninsa hukuncin daurin watanni goma a gidan kurkuku.

Rahoton ya ce kotu ta samu kamfanin Abdulrahman Bashir da laifin sabawa hukuncin da Alkali mai shari’a, Robin Knowles ya yi a cikin watan Satumban shekarar 2019.

KU KARANTA: Dauko ni haya aka yi domin in fallasa Magu - Lauya

Mai Rahamaniyya Oil and Gas Limited zai yi zaman kaso a Birtaniya
Kotu ta samu kamfanin Rahamaniyya Oil and Gas LTD da laifi
Asali: Twitter

A shari’ar da aka yi a bara, Alkali ya umarci kamfanin Rahamaniyya Oil and Gas Ltd ya mikawa wani kamfani da ake kira Energy Resource Ltd gangunan gas masu yawa.

Alhaji Abdulrahman Bashir wanda shi ne shugaban wannan kamfani na Rahamaniyya Oil and Gas, bai bada wadannan ganguna kamar yadda kotu ta bukace shi ba.

A hukuncin da Alkali ya yi yanzu, za a iya ragewa Bashir hukuncin daurinsa zuwa watanni shida idan har ya saduda, ya yi abin da aka bukace shi da ya yi tun farko.

Bayan haka an ci kamfanin man Rahamaniyya tarar fam £500,000 a dailin saba alkawari. Idan aka yi lissafi a kudin Najeriya wannan tara ta kai N250, 000, 000.

Jaridar ta ce Alkali ya kuma bukaci manajan wannan kamfani watau Adebowale Aderemi da ya biya tarar £10,000. A kudin gida, tarar ta haura Naira miliyan biyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng