Buhari ya amince da kashe N3.9bn domin kammala wasu aiyuka a jihohi biyar
Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta amince da kashe N3.9bn domin kammala aikin ginin sakatariyar tarayya a jihohin Anambra, Bayelsa, Nasarawa, Osun, da Zamfara.
Kazalika, FEC ta amince da kashe N1.5bn domin sake inganta haka Dam din Usuma da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.
Ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola, da takwaransa na birnin tarayya (FCT), Muhammad Bello, sun tabbatar da hakan yayin ganawarsu da manema labarai bayan kammala taron FEC.
Shugaba Buhari ne ya jagoranci taron FEC na yau, Laraba, da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo a fadar shugaban kasa.
Mista Fashola ya bayyana cewa an fara bayar da kwangilar aikin gina sakatariyar a kan kudi N13.5bn a shekarar 2011, inda ya kara da cewa an kara ware N3.9bn domin kammala aikin gaba daya a jihohin biyar wanda zai lashe jimillar kudi N17.4bn.
Ministan ya kara da cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta samarwa dukkan ma'aikatanta ofisoshin aiki a duk jihohin Najeriya.
Ya bayyana cewa har yanzu akwai sabbin jihohin da babu gine - ginen da ke zaman matsugunin wurin ma'aikatan tarayya saboda tsofin gine-ginen gwamnatin tarayya sun zama mallakar tsofin jihohi.
"An bayar da kwangilar aikin ne ga kamfanoni daban-daban har 16 kuma an fara aiki tun shekarar 2011, yanzu kuma mu ke burin mu kammalasu.
"Mun mika bukatar sake duba kudin kwangilar aiyukan sakamakon hauhawar farashin kaya da aka samu daga lokacin da aka fara bayar da kwangilar zuwa yanzu.
DUBA WANNAN: Sheikh Zakzaky ya raba magunguna da gidajen sauro a sansanonin 'yan gudun hijira
"Mu na son kammala wannan aiki na gina sakatariyar ma'aikatan gwamnatin tarayya a Anambra, Bayelsa, Nasarawa, Osun, da Zamfara," a cewar Fashola.
A nasa bangaren, ministan babban birnin tarayya, Abuja, ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta amince da kashe biliyan N1.5 domin kammala muhimmin aikin gina Dan din Usuma da ke yankin karamar hukumar Bwari.
Ministan ya bayyana cewa gina Dam din zai kawo yalwar ruwan fanfo a sassan Abuja na tsawon shekaru 30 ma su zuwa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng