Kwamitin tsare-tsare ya mikawa Sheikh Bala-Lau rahoton aikin Jami’ar As-Salam

Kwamitin tsare-tsare ya mikawa Sheikh Bala-Lau rahoton aikin Jami’ar As-Salam

Kungiyar Jama’atul Izatil Bidi’a wa Iqamatun Sunnah ta Najeriya, ta na shirin bude katafariyar jami’ar addinin musulunci a jihar Jigawa.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa kwamitin tsare-tsare da gudanarwa na kungiyar JIBWIS ta kammala aikin da aka bata, har ta gabatar da rahoto.

JIBWIS ta daurawa kwamitin Farfesa Umar Muhammad Labdo alhakin tsara yadda za a kafa jami’ar As-Salam Global University, jihar Jigawa.

Bayan kusan watanni biyu da wannan kwamiti ya zauna da shugabannin Jama'atu Izalatil Bid'a Wa'iqamatis Sunnah, ya gabatar da rahoto a makon jiya.

Shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya tabbatar da cewa sun karbi rahoton kafa wannan jami’a a Garin Hadejiya daga hannun kwamiti a Abuja.

An yi wannan zama ne babbar sakatariyar kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a Wa'iqamatis Sunnah da ke birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta.

KU KARANTA: Rade-radin mutuwa: Lauyoyin Sheikh Bala Lau sun rubuta takarda

Kwamitin tsare-tsare ya mikawa Sheikh Bala-Lau rahoton Jami’ar As-Salam
Takardun bude Jami’ar Musulunci ta Hadejiya
Asali: Twitter

Wannan rahoto ya kunshi kundin bayanai a game da harkar dokokin jami’a, binciken kyawun kasa, tsarin gini, da kuma sha’anin karantarwa.

Wadannan bincike za su taimaka wajen sanin dokokin kafa jami’a a Najeriya da kyawun kasar da ake shirin yin wannan gini, da kuma tsarin gini da aikin makarantar.

Mataimakin shugaban wannan kwamiti shi ne Ibrahim Sule. Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Farfesa Kabir Yusuf, Ahmed Ibrahim Lau, da Rabiu Idris Muhammad.

Wadanda su ka halarci zaman da aka yi wajen gabatar da rahoton sun hada da babban sakataren kungiya na kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe.

Sheikh Abdullahi Bala Lau da ya bada sanarwar wannan zama a shafinsa na Twitter, bai yi karin bayani game da wannan shiri da kungiyar addinin ta ke yi ba tukuna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel