Shugaban kasa 2023: Dandalin sada zumunta ya karade da fastocin yakin zaben Fayemi

Shugaban kasa 2023: Dandalin sada zumunta ya karade da fastocin yakin zaben Fayemi

- Saura kimain shekaru uku kafin a sake zaben shugaban kasa a Najeriya wato a 2023 kenan

- Tuni dai astocin kamfen din gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, na neman takarar wannan kujera ya karade soshiyal midiya

- Sai dai babban sakataren labaran gwamnan, Yinka Oyebode ya ce ubangidansa bai da masaniyar komai game da fastocin

Kimanin shekaru uku kafin zaben shugaban kasa na 2023, tuni fastocin kamfen din gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, na neman takarar wannan kujera ya karade soshiyal midiya.

Shugaban karamar hukumar Ikere na jihar Ekiti, Mista Femi Ayodele ne ya dauki nauyin fastocin mai dauke da hotonsa kuma a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Fastocin wanda aka gano a shafukan soshiyal midiya ya haddasa muhawarar siyasa a shafuka daban-daban.

Fastocin sun nuno Fayemi sanye da babbar riga shudi da hular Awolowo, jaridar The Nation ta ruwaito.

Shugaban kasa 2023: Dandalin sada zumunta ya karade da fastocin yakin zaben Fayemi
Shugaban kasa 2023: Dandalin sada zumunta ya karade da fastocin yakin zaben Fayemi Hoto: The Nation
Asali: UGC

Sakon da ke jikin fastocin dauke da logon APC ya ce: “Ku marawa Mai girma Dr. John Kayode Fayemi baya don zama shugaban kasa a 2023."

Da yake tabbatar da fastocin, Mista Ayodele, ya ce ya buga su ne domin nuna goyon baya da biyayyarsa ga Gwamna Fayemi sabanin hasashen cewa yana yi masa yankan baya.

KU KARANTA KUMA: An yanke hukuncin kisa ga barawon doyar da ya kashe mai gona

Ya ce gwamnan ya cancanci hawa wannan kujera duba ga tarin iliminsa, nasarorin shugabancinsa da kwarewarsa a siyasa.

Ya kara da cewar jajircewar Fayemi, hikimarsa da kwarewarsa sun sa ya cancanci jagorantar Najeriya a zabe na gaba.

Amma da aka tambaye shi kan ci gaban, babban sakataren labaran gwamnan, Yinka Oyebode ya ce ubangidansa bai da masaniyar komai game da fastocin.

Oyebode, wanda yace jagoran buga hotunan na nuna ra’ayin kansa ne ya bukaci jama’a da kada su damu da shi.

Ya kara da cewar ubangidansa ya mayar da hankali ne ga jagoranci da yadda zai bunkasa Ekiti ta bangaren more rayuwa, tattalin arziki da ci gaban jama’a maimakon lamuran da ke kewaye da zaben 2023.

A baya babban hadimin gwamnan kan sadarwa, Segun Dipe, a ranar 5 ga watan Mayu ya karyata cewar Fayemi na tarairayan zama shugaban kasa a 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel