An nadi bidiyon ‘Yaran Magu’ suna neman toshiyar bakin N75m daga hannun ɗan kasuwa
- Wani ɗan kasuwa, Donald Wokoma, ya shaidawa kwamitin binciken Salami cewa 'yaran Magu' sun nemi ya basu toshiyar bakin 75m
- Kwamitin bincike ta Mai Shari'a Salami ce ke gudanar da bincike a kan zargin rashawa da ake yi wa Magu
- Wokama ta gabatar da takardar rantsuwa da ke nuna ya rubuta takardar ƙorafi a kan 'yaran Magu' kafin su rufe asusun bankin sa
Wani rahoto da PRNigeria ta wallafa ya ce an nuna wa kwamitin bincike na shugaban ƙasa karkashin jagorancin Mai Shari'a Salami wani faifan bidiyo inda jami'an EFCC da aka fi sani da 'Magu Boys' wato Yaran Magu suka nemi wani ɗan kasuwa ya basu toshiyar baki na N75.
Legit.ng ta ruwaito cewa rahoton ya nuna ɗan kasuwan, Donald Wokoma na kamfanin Damijay Integrated Services Limited ya gabatar da takardar rantsuwa da ke nuna cewa ya rubuta takardar ƙorafi a kan 'Yaran Magu' kafin suka rufe asusun bankin sa.
A cewar rahoton, EFCC a 2018 ta ƙi bin umurnin da Mai Shari'a O.C. Agbaza ya bayar na cewa a buɗe asusun bankin Dimijay Services Limited bayan kamfanin ta shigar da ƙarar a cewa ana take mata hakokinta a kotun Abuja.
Wani lauya mazaunin Abuja, Victor Giwa wanda ake zargin yana da hannu cikin karbar rashawar ya amince cewa muryarsa ce aka ji a cikin bidiyon mai tsawon minti 27 da aka nuna wa kwamitin binciken.
DUBA WANNAN: Kungiyar ISWAP ta yi garkuwa da mutane masu dimbin yawa a Borno
An ji muryar Giwa, tsohon lauyan kamfanin da EFCC ke bincike a kai ya ambaci sunan dakataccen shugaban EFCC, Ibrahim Magu da wasu jami'an da ke zargi da rashawa.
Kafar watsa labaran ta ruwaito cewa ɗan kasuwan ya yi iƙirarin cewa a ranar 20 ga watan Mayun 2020, Giwa ya bukaci a saka hannu a kan wasu chek ɗin kuɗi uku kowannensu na Naira miliyan 25 idan har yana son a buɗe masa asusun bankin kamfanin sa.
Wanda ya shigar da ƙarar ya bayyana cewa 'Yaran Magu' sun bayar da asusun bankuna uku da za a tura musu kudaden kamar haka; Cikin Gida Nigeria Limited: 1771773211, Black and Global Concept Limited; 0259011841 da Amina Kigbu mai lamba 2176716071.
Da bankin suka ƙi karɓar ki chek ɗin sai 'Yaran Magu' suka bukaci ɗan kasuwar ya tura kudaden da kansa zuwa asusun bankunan guda uku.
A cewar takardar rantsuwa da aka gabatar, Yaran Magu sun bukaci a biya su kashi 40 cikin dari na kudin da ke asusun ajiyar banki na kamfanin da ya kai Naira miliyan 100 amma ɗan kasuwar ya ƙi amincewa nan take.
Bayan ya ƙi amincewa ya biya kudin, ɗan kasuwan ya ce, "Wani Mr Mohammed Goje na EFCC a ranar 9 watan Yulin 2020 ya kira ni ya ce in zo ofishin su a ranar 10 ga watan Yuli.
"Na amsa gayyatar na jira har zuwa karfe 5.09 na yamma na tafi sai ya aiko min da sakon tes cewa an yi kara ta kotun Abuja a Lugbe karfe 8.30 na safiyar Litinin don a gurfanar da ni.
"Ya yi min gargadi a sakon tes cewa in zo kotun idan bana son a ci mun mutunci. 'A ranar 13 ga watan Yuli da na tafi kotun Lugbe an bani wata takardar ƙarar da aka shigar ranar 19 ga watan Yunin 2020 (kwanaki biyu bayan na ƙi amincewa in biya rashawar kashi 40 na kuɗin da ke asusun kamfani na).
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng