Rigimar siyasa: Jami’an ‘Yan Sanda sun gayyaci Bakwana domin yi masa tambayoyi

Rigimar siyasa: Jami’an ‘Yan Sanda sun gayyaci Bakwana domin yi masa tambayoyi

Mataimakin sufeta janar na ‘Ya sanda mai kula da shiyyar Kano ya gayyaci mai ba gwamnan Kano shawara, Mustapha Bakwana, domin ya amsa wasu tambayoyi.

Alhaji Mustapha Bakwana shi ne babban mai ba mai girma gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje shawara a kan harkokin siyasa a jihar Kano.

Daily Nigerian ta fitar da rahoto cewa an ga Mustapha Bakwana a wani bidiyo ya na nuna bindiga, sannan ya na tunzura wasu matasa a wajen taron sulhun jam’iyyar APC.

Jaridar ta ce ana zargin cewa wadannan matasa, magoya bayan ‘dan siyasar ne. A wannan bidiyo, Mustapha Bakwana ya yi kira ga mutanen na sa su hallaka ‘yan adawa.

Kwamitin sulhu na jam’iyyar APC wanda Rt. Hon. Kabiru Rurum ya ke jagoranta a jihar Kano ya yi wani zama a makon da ya gabata a karamar hukumar Kumbotso.

Bayan jini-da-majinan da aka yi tsakanin wasu matasa da yaran Bakwana a wajen wannan taro na APC, an sanar da jami’an tsaro game da abin da ya ke aukuwa a jihar.

KU KARANTA: Gwamnoni, sojoji, Ministoci Sanatoci, Sarakai, da su ka rasu a 2020

Rigimar siyasa: Jami’an ‘Yan Sanda sun gayyaci Bakwana domin yi masa tambayoyi
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje
Asali: UGC

Sai dai a wata hira da Mustapha Bakwana ya yi a gidan rediyon Freedom a Kano, ya musanya wannan zargi, ya ce abokan adawa ne su ka kirkiri bidiyon da ake magana.

Bakwana ya wanke kan shi a lokacin da aka tattauna da shi gidan rediyon, ya zargi masu yi masa hassada saboda irin nasarar da ya ke samu a tafiyar siyasa da kitsa wannan bidiyo.

Da aka tuntubi kakakin ‘yan sanda na shiyyar Kano, Rabilu Ringim, ya tabbatar da cewa su na binciken mai ba gwamnan shawara game da zargin da aka jefe shi da su.

Zargin da ke kan wuyan hadimin gwamnan na Kano sun hada da fito da karamar bindiga da amfani da yara da munanan makamai wajen tada zaune tsaye a cikin al’umma.

Wannan ne karo na biyu da ake tuhumar wani mukarrabin gwamna Ganduje da laifi. A makon jiya kun ji ana zargin Ali Baba Fagge da yin sama da fadi da kudin addu’o’i.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng