Yan bindiga sun kashe sojoji 3 da 'dan sa kai 1 a Niger

Yan bindiga sun kashe sojoji 3 da 'dan sa kai 1 a Niger

- ‘Yan fashi a Neja sun kashe sojojin Najeriya uku da wani dan kungiyar ‘yan banga guda a jihar

- An kashe sojojin da dan bangan ne a lokacin wani musayar wuta tsakaninsu da ‘yan fashin

- Sun je ceto wani dan kasar China da direbansa da ‘yan bingidan suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Rafi da ke jihar

Wani rahoto daga jaridar Daily Trust ya nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe sojoji uku da wani dan banga daya a Yakila, karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja.

‘Yan bindigan sun yi garkuwa da wani dan kasar China da direbansa a wani wurin da suke aikin gini a kauyen sannan suka tsere da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

A cewar rahoton, sojojin da dan bangan sun yi kokarin ceto dan Chinan da direbansa ne lokacin da aka kashe su a wani musayar wuta.

Wani idon shaida da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa sun rasa rayukansu a wani musayar wuta da suka yi da ‘yan bindigan wanda yawansu ya kai kimanin 30.

Shaidan ya ci gaba da bayyana cewa ‘yan fashin na da makamai sosai sannan sun gudanar da farmakin ne a kan Babura 15.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari (ga batutuwa uku da suka tattauna a kai)

Wani hadimin gwamnan jihar Neja kan lamuran tsaro, Kanal MK Maikundi (ritaya) ya tabbatar da lamarin, cewa an tura hukumomin tsaro domin magance lamarin.

A wani labarin kuma, mun ji rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Katsina sun kama wasu mutane da ake zargin su na taimakawa miyagun da su ke addabar Bayin Allah.

Jaridar Katsina Post ta ce jami’an tsaron sun yi ram da masu karbar dabbobin sata daga hannun ‘yan bindigan da su ke shiga kauyukan Katsina su na yin ta’adi.

Sakamakon wannan nasara da ‘yan sanda su ka yi, sun karbe dabbobi daga hannun wadanda ake zargi da agazawa ‘yan bindigan wurin yin gaba da dukiyar mutane.

Gambo Isah ya ce wadannan mutane da aka kama, su na da niyyar saida dabbobin ne a kasuwa. “Bincike ya na cigaba da wakana.” Inji jami’in ‘yan sandan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel