Na’urorin hakon rijiyoyin mai sun ragu daga 21 zuwa 6 a watanni 5

Na’urorin hakon rijiyoyin mai sun ragu daga 21 zuwa 6 a watanni 5

A lokacin da kamfanonin mai da-dama su ke fama da barazanar tattalin arziki a Duniya, aikin hako mai da ake yi a Najeriya ya gamu da kalubale a halin yanzu.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa kayan hako danyen man da ake amfani da su a kasar nan sun farra cinyewa. Najeriya ta na kokarin hako rijiyoyi ne a yankin Arewa.

Adadin na’urorin da su ke aikin bincike da hako mai a Najeriya sun ragu da kashi 33.33% daga watan Yuni zuwa Yuli.

Alkaluman da jaridar ta samu daga kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin mai sun tabbatar da cewa na’urorin da su ke aiki sun ragu daga tara zuwa shida.

A cikin watan Maris, Najeriya ta na da lafiyayyun na’urorin hako mai har 21, zuwa watan Afrilu adadin na’urorin su ka sauka zuwa 16.

Kamar yadda OPEC ta bayyana, takwas daga cikin wadannan na’ura sun tashi aiki a watan Mayu, aka bar ma’aikatan kasar su na fama da takwas.

Rahoton ya ce raguwar kayan aikin na nuna kokarin da ake yi wajen lalube da yunkurin hako sababbin rijiyoyin danyen mai da gas a jihohin Najeriya.

KU KARANTA: An samu fetur a Filato

Na’urorin hakon rijiyoyin mai sun ragu daga 21 zuwa 6 a watanni 5
Ana hako sababbin rijiyoyin mai a Najeriya
Asali: UGC

Ga wadanda ba su sani ba, ana amfani da wadannan manyan na’urori ne wajen huda kasa domin a cin ma ruwa ko sauran ma’danai kamar danyen mai.

Bayan tsawon lokaci ana aiki da wadannan na’urori, a kan cinye karfinsu ta yadda sai an nemi wasu.

Kamfanin Seplat mai aiki a Najeriya ya sanar da cewa ya kawo sababbin dabaru domin rage kashe kudi da akalla 30% domin gujewa tafka asara a kasuwa a karshen shekarar nan ta 2020.

Wannan kamfani ya ce: “An dakatar da aikin hako rijiyoyin mai, ana duba duk wasu kashe-kashen kudi wajen yin aikin da ba su zama tilas ba a wuraren da ake neman danyen mai.”

Shugaban kungiyar masana harkar mai na kasa, Joseph Nwakwue, ya ce babu alamun cewa kasuwa za ta yi kyau nan gaba sakamakon annobar COVID-19 da ake fama da ita.

Abubuwa ba su tafiya daidai kamar yadda kamfanonin mai su ke so. Farashin gangar danyen mai ya karye a Duniya, wannan ya karyawa masu aikin mai kwarin gwiwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel