Yadda Abacha ya kamani ya daure a 1995 bayan na ki daukan shawarar Carrington - Obasanjo
A ranar Talata ne tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa, marigayi janar Sani Abacha, ya kamashi ya daure a kurkuku bayan ya ki daukan shawarar tsohon jakadan kasar Amurka a Najeriya, Walter Carrington.
A cikin wata wasikar ta'aziyya da Obasanjo ya aikawa Arese Carrington, uwargidan marigayi Carrington, ya bayyana cewa tsohon jakadan ya yi ma sa tayin ya yi gudun hijira zuwa kasar Amurka a lokacin da suka hadu a wurin wani taro.
Obasanjo ya bayyana cewa sun hadu da tsohon jakada Carrington a birnin Copenhagen a wurin wani taron kasa da kasa da majalisar dinkin duniya ta shirya a lokacin.
Tsohon shugaban kasar ya ce Carrington ya bashi tabbacin samun matsuguni da kariyar kasar Amurka domin kubutar da shi daga ukubar gwamnatin Abacha.
A cikin wasikar sakon ta'aziyyar, wanda kakakinsa, Kehinde Akinyemi, ya rabawa manema labarai, Obasanjo ya bayyana cewa har abada zai kasance mai godiya ga iyalin Carrington saboda irin damuwar da ya nuna a kansa.
"Ba zan taba mantawa da haduwarmu a wurin taron majalisar dinkin duniya ba a birnin Copenhage a shekarar 1995, lokacin ina zaman jakadan majalisar dinkin duniya a kan harkokin cigaba.
"Ya yi min gargadi tare da yi min tayi mai tsoka, shawara da gargadin da Ambasada Carrington ya yi min sun tabani matuka.
"Ya kirani gefe guda a Copenhagen tare da sanar da ni cewa gwamnati na shirin kamani da zarar na koma Najeriya, a saboda haka kar na sake na koma gida.
DUBA WANNAN: An sake kai wa tawagar wani gwamnan APC harin bindiga, an kama mutane 15
"Bai tsaya iya nan ba, ya yi min tayin cewa gwamnatinsa ta kasar Amurka za ta bani wuri na fake a matsayin dan gudun hijira.
"Duk da irin tsoka da tabbacin da tayinsa ya kunsa, na ki karba, ban yi aiki da shawarar da Ambasada Carrington ya bani ba.
"Bayan na dawo gida Najeriya, Abacha ya kamani ya tsare a gidan yari.
"Hatta a lokacin da na ke a tsare a gidan yari, Ambasada Carrington ya cigaba da ziyartar mata ta domin ganin halin da take ciki da kuma jin halin da nake ciki a gidan yari.
"Tabbas ya kasance aboki nagari da zan cigaba da yin alfahari da shi koda yaushe," a cewar Obasanjo.
Obasanjo ya yi alhini tare da mika sakon ta'aziyya da jimamin rashin Ambasada Carrington ga matarsa, kasar Amurka, da duniya baki daya ta yi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng