An sake kai wa tawagar wani gwamnan APC harin bindiga, an kama mutane 15
'Yan sanda a jihar Imo sun sanar da cewa sun kama mutane 15 da ake zargin suna da hannu a harin da aka kai wa gwamnan jihar, Hope Uzodinma, ranar Litinin.
An kaiwa gwamnan harin ne yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa bude wata mashaya da gwamnatinsa ta ginawa sojoji a cikin barikinsu ta 34 Attilary da ke Obinze.
Batagarin matasa dauke da makamai sun kai wa tawagar gwamnan hari ta hanyar fakewa da zanga-zangar neman biyansu basukan albashin wata uku a matsayin ma'aikatan hukumar jihar Imo da ke kula da cigaban sassan jihar da ke da arzikin man fetur (ISOPADEC).
Gwamnatin Imo ta bayyana cewa 'yan adawa ne suka dauki nauyin mafi yawan masu zanga-zangar, kamar yadda wani jami'in gwamnatin jihar ya yi ikirarin cewa bincike ya nuna.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Imo, Isaac Akinmoyede, ya ce mutanen da su ka kama sun yi ikirarin cewa su ma'aikatan hukumar ISOPADEC ne da ke zanga-zanagr neman biyansu bashin albashi na tsawon watanni uku da suke bin gwamnati.
Ya kara da cewa an kamasu da wata karamar bindiga guda daya, adda guda biyu, takunkumin rufe fuska, da kuma kwadon rufe kofa.
"Sun yi amfani da karamar abindigar da kuma manyan wukakensu wajen kai wa motocin tawagar gwamna hari," a cewar kwamishinan.
DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamnatin tarayya ta magantu kan lokacin bude jami'o'i
A cewar kwamishinan, babu asarar rayuka sakamakon harin da matasan suka kaiwa tawagar gwamnan a daidai yankin 'Concord' da ke New Owerri.
"Sai dai, matasan sun lalata gilasan motoci tare da lalata wasu daga cikin motocin da ke tawagar gwamnan," a cewarsa.
Kwamishinan ya kara da cewa an mika wadanda aka kama zuwa sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng