Gwamnatin Najeriya za ta kashe N12.658trn a kasafin 2021 - Minista Zainab Ahmed

Gwamnatin Najeriya za ta kashe N12.658trn a kasafin 2021 - Minista Zainab Ahmed

Gwamnatin tarayya za ta kashe naira tiriliyan 12.658 a matsayin kasafin kudin shekarar 2021.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sabuwar takardar mahangar tattalin arziki da ma’aikatar kudi, kasafi, da tsare-tsare ta fitar.

Takardar, mai dauke da sa hannun ministar kudi, Zainab Ahmed, ta nuna cewa adadin ya samu karin kaso 17.2 na kasafin kudin 2020; naira tiriliyan 10.8, da aka sake nazari daga baya.

Gaba daya jimillar kudaden shiga da ke kasa na kasafin kudin shekara mai zuwa an kimanta shi a kan naira tiriliyan N7.498 yayinda jimillar kudin da za a kashe an kiyasta shi a kan naira tiriliyan N12.658.

A daya bangaren, jimillar kudin da za a kashe ya hada da naira biliyan N481.41 na kudaden da aka yi hada-hadarsu, ana bin kasar bashin naira tiriliyan N3.124, sai kudin da aka ware don biyan bashin naira biliyan N220.

Naira tiriliyan N5.746 zai tafi a kudin fansar kaya da ayyuka, sannan an kuma ware naira triliyan uku a matsayin kudaden gudanar da manyan ayyukan raya kasa.

Daga cikin kudaden ayyukan, ma'aikatu, sassa da hukumomi za su ja naira tiriliyan N1.485.

Ma'aikatar ta yi bayanin cewa kiyasin ayyukan ya yi daidai da kundin tsarin kasafin kudin gwamnati na 2021 zuwa 2023.

Gwamnatin Najeriya za ta kashe N12.658trn a kasafin 2021 - Minista Zainab Ahmed
Gwamnatin Najeriya za ta kashe N12.658trn a kasafin 2021 - Minista Zainab Ahmed
Asali: Twitter

Ministar ta kara da cewa an tsara manyan kididdigar kundin kasafin kudin na 2021 zuwa 2023 daidai da mahangar tattalin arzikin duniya da na cikin gida.

Naira biliyan N481 da aka ware zai tafi zuwa ga majalisar shari’a ta kasa (NJC), hukumar ilimi (UBE), hukumar ci gaban yankin Neja Delta (NDDC), majalisar dokokin tarayya (NASS), hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC).

Sai hukumar kare hakkin bil-adama na kasa (NHRC), hukumar sauraron korafe-korafen jama’a (PCC), hukumar ci gaban arewa maso gabas (NEDC) da kuma hukumar BHCPF.

KU KARANTA KUMA: Batanci ga Annabi: Majalisar shari'ar Musulunci ta bukaci Ganduje ya sa hannu don rataye Sharif

Ana tsammanin wadannan bangarori na gwamnati da hukumomi za su yi amfani da kudaden don abubuwan da aka tanadar.

Ana kuma bukatar dukkanin wadanda suka amfana da wannan kudi su bayar da rahoto na kudin da aka basu da kuma yadda suka kashe kudaden da suka karba daidai da dokar kashe kasafin kudi na 2007.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel