Jerin fitattun mutanen da su ka riga mu gidan gaskiya a bana

Jerin fitattun mutanen da su ka riga mu gidan gaskiya a bana

A wannan shekara da ake ciki, babu shakka Najeriya ta rasa manyan mutane; daga ma’aikatan gwamnati, tsofaffin wadanda su ka rike mukamai, zuwa masu sarautar gargajiya.

Legit.ng Hausa ta kawo wasu daga cikin wadanda su ka rasu a wannan shekarar:

1. Abba Kyari

Abba Kyari ya na cikin wadanda COVID-19 ta kashe a Najeriya. Kafin mutuwarsa shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

2. Ismaila Isa Funtua

Kwanan nan ISamaila Isa wanda na-hannun daman shugaban kasa ne ya cika bayan gajerar jinya.

3. Buruji Kashamu

COVID-19 ta kashe gawurtaccen ‘dan siyasar adawa na kasar Yarbawa, Sanata Buruji Kashamu.

4. Abiola Ajimobi

Wani wanda Coronavirus ta kashe a shekarar nan shi ne tsohon gwamnan Oyo Abiola Ajimobi.

5. Amb Wilberforce Juta

A watan Agusta ne tsohon Gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Amb Wilberforce Juta ya rasu.

6. Alhaji Wada Maida

Tsohon sakataren Muhammadu Buhari kuma shugaban ma’aikatara NAN, Wada Maida ya cika a bana.

7. Bayo Osinwo

Sanatan Legas Bayo Osinwo ya rasu kwanaki, jim kadan bayan nan Hon. Tunde Braimoh ya mutu.

8. Rose Oko

Rose Oko wanda ita ma kafin ajalinta ‘yar majalisar Kuros-Riba ce ta rasu a farkon shekarar nan.

9. Inatius Datong Longjan

Sanata Datong Longjan mai wakiltar Filato ta kudu a majalisar dattawa ya rasu a watan Fubrairu.

10. Bamidele Ishola Olumilua

Gwamnan tsohuwar jihar Ondo watau Bamidele Isola Olumilua ya rasu ya na da shekara 80.

KU KARANTA: Wani Hakimi ya na dauke da COVID-19 a Kaduna

Jerin fitattun mutanen da su ka riga mu gidan gaskiya a bana
Ismaila Funtua ya rasu kwanaki Hoto: Twitter
Asali: Twitter

11. Tolulupe Arotile

A watan jiya ne Tolulupe Arotile ‘yar shekara 24 mai tuka jirgin yakin Najeriya ta rasu a hadari.

12. Ayo Fasanmi

Tsohon ‘dan siyasar nan Ayorinde Fasanmi ya cika a kusan shekaru 95 a karshen watan Yuli.

13. Richard Akinjide SAN

A bana ne tsohon Ministan ilimi da sharia na tarayya, Cif Olusale Richard Akinjide ya bar Duniya.

14. Dr. Hallliru Alhassan

Halliru Alhassan wanda ya taba rike kujerar ministan lafiya ya rasu a watan Mayun bana.

15. Sam Momah

Janar Sam Momah, tsohon sojan da ya yi ministan kimiyya da fasaha a gwamnatin tarayya ya mutu.

16. Samaila Iliya

Wani soja da aka rasa a shekarar nan shi ne Manjo Janar Samaila Iliya, ya cika ne a makon jiya.

17. Inuwa Abdulkadir

Daga cikin wadanda aka rasa akwai Inuwa Abdulkadir, jigon jam’iyyar APC kuma tsohon minista.

18. Orho Obada

Janar Orho Obada mutumin jihar Delta ne wanda ya taba yin minista na ayyuka, ya rasu a bana.

19. Alhaji Ganiyu AbdulRazaq

Ganiyu AbdulRazaq mahaifin gwamnan Kwara ne mai-ci, kuma babban lauyan farko a Arewa.

20. Tafida Abubakar Illa

Mai martaba Sarkin Rano, Tafida Abubakar Illa ya rasu kwanaki. Sarkin ya rasu ne a wani asibiti a Kano.

[Akwai yiwuwar a samu wasu fitattun da su ka rasu kwanan nan da mu ka manta mu ambace su.]

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel