Dole ne mu shawo kan rashin tsaro, ko kuma mu fuskanci matsala - Masari
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya samu tattaunawa da jaridar Daily Trust a kan garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran matsalolin tsaro da suka yi katutu a jihar Katsina.
Ya yi bayanin nasarorin da ya samu a yayin da ya cika shekaru biyar a kujerar gwamnan jihar.
Kamar yadda gwamnan ya bayyana, "A lokacin da muka hau mulki, mun yi kokari wurin kawo sabbin tsare-tsare a fannin Ilimi, lafiya, noma da kiwo, samar da ruwa, tsaro da sauran ababen more rayuwa.
"Mun dauki alkawarin cewa za mu daga kudin da ake warewa fannin ilimi duk shekara kuma mun yi. Mun daga na fannin lafiya shima.
"A cikin shekaru biyar da suka gabata, da gudumawar SUBEB da UBEC, da gudumawar gwamnatin jihar, an gyara makarantun sakandare tare da gina wasu.
"Mun diba malaman firamare da sakandare a kalla 5,000. A yanzu mun kirkiro shirin S-Power wanda muka dauki malamai 5,000 wadanda muke biya 20,000 a kowanne wata.
"A bangaren lafiya, mun gyara manyan asibitocin Katsina, Funtua da Daura. Ba mu son ganin marasa lafiyanmu suna zuwa Zaria, Kano ko Sokoto saboda rashin kayan aiki."
Masari ya kara da cewa, "Babbar matsalarmu a yau ita ce matsalar tsaro, wacce muka fuskanta tun kafin mu hau mulki. Amma kuma annobar korona ta sake bada damar hauhawar matsalar. Hakazalika, ta tsayar da mu wurin biyan albashi.
"Babbar matsalar shine yadda korona ta fadar da farashin man fetur, wanda hakan ya shafi asusun bankin kasar.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya ja kunnen 'yan Najeriya a kan tada tarzoma
"Hakazalika, dole ne mu yi amfani da kudaden wurin taimaka wa 'yan sanda da sojoji wurin yakar ta'addanci. Ina goyon bayan gwamnonin da ke kira ga gwamnatin tarayya da ta bada tallafi wurin tsaro.
"Har yanzu muna da 'yan gudun hijira a Batsari, ba a maganar wadanda suka zauna da 'yan uwansu."
A baya mun ji cewa gwamna Masari a ranar Lahadi ya wanke shugaba Muhammadu Buhari daga zargin barin tabarbarewar tsaro a jiharsa da kuma Arewa maso Yamma.
Shugaban kasa ya yi duk mai yiyuwa don dai daita lamura a shiyyar, a cewarsa, yana mai nuni da cewa rundunar soji ne suka gaza amfani da kokarin shugaban kasar wajen cimma nasara.
Masari ya bayyana hakan ne a taron raba tallafin miliyan goma ga mata 1,000 da kuma tallafin karatu na miliyan bakwai ga dalibai 701 daga karamar hukumar Rimi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng