Aron $33bn: Takardun Rotimi Amaechi sun banbamta da na ‘Yan Majalisa
Wasu kwamitocin majalisar wakilan tarayya su na binciken duk kwangiliolin da kamfanonin waje su ke yi ko bashin da gwamnatin Najeriya ta karbo daga ketare.
A ranar Litinin, 17 ga watan Agusta, 2020, kwamitocin yarjejeniya da bin ka’idojin aiki na majalisar wakilai ya samu sabani da ministan sufuri na kasa.
Jaridar Premium Times ta ce Majalisa ta sha ban-bam ne da Rotimi Amaechi a kan kudin yarjejeniyar kwangilar da ma’aikatar sufuri ta shiga da kasar Sin.
Shugaban wannan kwamiti, Nicholas Ossai ya zargi ma’aikatar da sa hannu a kan yarjejeniyar fam Dala biliyan 33 ba tare da samar da yadda za a fito da kudin ba.
Honarabul Nicholas Ossai ya yi wannan jawabi ne a lokacin da majalisa ta saurari wannan batu a ranar Litinin, ya ce dole sai sun tantance kafin a rika amincewa da bashi.
Ossai ya ce sun kawo wannan bincike ne domin warware duhun da ake ciki game da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta shiga da kasashen waje.
KU KARANTA: Tsohon Sakataren Buhari ya cika
‘Dan majalisar ya ce akwai yarjejeniyar bashi da hadin-kai fiye da 500 da Najeriya ta shiga da gwamnatocin kasashe da kamfanonin ketare.
“Daga takardun da mu ka samu, mun ga cewa ma’aikatar sufuri kawai ta shiga yarjejeniyar Dala biliyan 33 ba tare da cikakken tsarin tattalin arziki ba.” Inji Ossai.
Ya ce: “Wadannan yarjejeniya ba su yi la’akari da arzikimu na gida ba, sannan babu shaidu, da takamaimen hukumomin gwamnati da su ka tsaya a kai.”
Majalisar wakilan ta ce akwai alamar tambaya game da kashi 15% na kudin aiki da ake fara biya. “Ya zama dole mu yi tambayayoyi da nufin samun amsoshi da za su gyara tsarin.”
Rt. Hon. Amaechi ya ce tun da shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki, yarjejeniyar bashi daya rak gwamnati ta shiga da kasar Sin, na aron fam Dala biliyan 1.6.
Akwai mutanen Najeriya fiye da 20, 000 da Sinawa 560 da su ke cin abinci da aikin dogon da ake yi. Sannan ya ce gwamnatin PDP ce ta karbo aron Dala miliyan 800.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng