Rayuwarmu cikin Sambisa a lokacin da aka kama mu – Daga bakin wadanda su ka tsero

Rayuwarmu cikin Sambisa a lokacin da aka kama mu – Daga bakin wadanda su ka tsero

Renata Yohanna da wasu ‘yanuwanta biyu sun bar gida ne a kauyen Tugunshe, karamar hukumar Konduga da nufin zuwa gona, amma su ka kare a hannun Boko Haram.

Daga kokarin yin huda a gona, Yohanna, Luka Jato da kuma Lami Jato sun koma neman hanyar da za su tsere daga hannun ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

A 2014, Boko Haram sun sace kakannin wadannan Bayin Allah, har sai da su ka shafe shekaru uku a tsare. Wannan ya sa ganin ‘yan ta’addan ya raza wadannan mutane farat daya.

‘Yan ta’addan sun shigo gonakinsu ne dauke da kayan sojoji da makamai, nan ta ke kowa ya kidime, ya fara neman yadda zai tsere, amma a karshe aka yi ram da mutane takwas.

“Ba mu gane abin da ya ke faruwa ba, mun ga kowa ya na gudu, har da direban tarakta ya nemi ya tsere.”

“Sun karbe wayoyi da kudinmu, sannan su ka fada mana cewa za su kyale maza hudu har da Luka Jato, amma za su tafi da direban tarakta da mata biyu.”

Renata ta shaidawa jaridar Daily Trust a hirarsu cewa daya daga cikinsu ta yi ta zabga kuka. Da ‘yan ta’addan su ka tambayi addininsu, sai su ka fada masu cewa su kiristoci ne.

“Ya tambayi ya aka yi na zama kirista ba musulma ba domin na yi kama da kyakkyawar macen musulma. Na fada masa haka Ubangiji ya yi ni, kamar yadda ya yi shi musulmi.”

Renata ta ce daga nan aka zarce da su zuwa kauyen Markas. Su ka ci abinci, su ka gana da Amir watau shugaban ‘yan ta’addan har ya ba ta magunguna da bargo da ta ce ba ta jin dadi.

KU KARANTA: Mun yi wa Buhari kokari amma bai kawowa Arewa zaman lafiya ba

Rayuwarmu a cikin Sambisa bayan an kama mu – Daga bakin wadanda su ka tsero
Janar Buratai da Shugaban kasa Buhari
Asali: Depositphotos

A nan aka bukaci su yi sallah, su ka shaida masu su kiristoci ne. Bayan nan ne aka fada masu za a kai su gaban shugabannin kungiyar, ashe dajin sambisa za a shiga da su.

“Mun shafe kwanaki biyu mu na tafiya a titi. Titin babu kyau, amma sun iya kutsawa da babur. Da mu ka zo Mafa, sai mu ka kwana mu ka huta, washegari mu ka cigaba da tafiya.”

Da isa sambisa, Renata ta ce ta yi mamakin ganin yadda Boko Haram su ke aiki. “Sun kafa shige kala-kala."

Ta ce Boko Haram su na da tsari a cikin daji, ‘yan ta’addan su na dauke da kayan sojoji, JTF, ‘yan sanda da sauransu.

“A karshe mu ka isa gidan wani Amir wanda ya ce mani ina da kyau, ko ni mai dakin Buratai ce ko IGP. Na fada masa daga gona aka dauko ni, ina da aure da ‘ya ‘ya. Ya yi mani alkawari ba zai kashe mu ba, ganin na tsorata”

“Washegari mu ka fara jin kara ta ko ina, mu ka yi ta kuka. Wata daga cikin matan Amir su ka fada mana mu daina kuka domin sun saba da irin wannan."

Lami ta ce abin dai babu dadi, aure kuwa kullum cikin yin sa ake yi a dajin, ga kuma yawan haihuwa saboda tarin mata. Ta ce an yi yunkurin canza masu addini kafin a sake su.

“Sun tuntubi ‘yanuwanmu ta wayoyinmu, wata rana kwatsam aka ce mana mu shirya. Mahaifiyarmu ta kwana a daji ta na jiranmu, aka biya kudi aka sake mu.”

A dajin Sambisa akwai kabilu da dama kamar; Shuwa Arab, Marghi, Fulani, Hausa, amma Kanuri sun fi yawa inji Lami.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel