Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da Oshiomhole
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin ganawa da tsohon Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole
- Manyan jiga-jigan na APC biyu na ganawa ne a fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya
- Ba a san dalilin ganawar tasu ba amma ga dukkan alamu baya ras nasaba da hasashen jigon jam'iyyar na cewa wasu na kulla-kullan dawo da Oshiomhole kujerarsa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin ganawa da tsohon Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole.
Manyan jiga-jigan na APC biyu na ganawa ne a fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya, Abuja.
An gano Oshiomhole cikin shigarsa ta al’ada tare da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Cif Ibrahim Gambari.
Da isar su kai tsaye suka wuce ofishin shugaban kasar.
Ba a san dalilin ganawarsu ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
A baya dai mun kawo maku cewa, darakta janar na kungiyar gwamnonin APC, Dr Salihu Lukman, ya zargi cewa akwai shirin mayar da Adams Oshiomhole tsohuwar kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar APC.
Ya yi ikirarin cewa akwai kokarin da ake yi don zagon kasa ga kwamitin rikon kwarya na Mai Mala Buni.
DG Lukman a wani bayani da yayi a kan kwamitin rikon kwaryan, ya ce: "komai ana yin shi ne don ganin an juya siyasar cikin gida don samun yadda Oshiomhole zai haye kujerar shugabancin jam'iyyar."
Lukman, wanda babban mai adawa ne da salon Oshiomhole, ya ce daga cikin wani bangare na kokarin shine amfani da zaben Edo wajen cin zarafin shugabannin APC.
KU KARANTA KUMA: Mutuwar Janar Iliya: Buhari ya yi alhini, ya aika sako zuwa rundunar soji
"Amma wannan bai kamata ya zama matsala ba. Amma kuma, ganin cewa ana amfani da wasu salo ne don bacin suna da cin zarafi shugabannin jam'iyyar don wata manufa a zaben Edo ne abun takaici.
"Abun da ya fi zama na damuwa shine yadda Oshiomhole da wasu magoya bayansa basu son tunkarar zaben Edo a kan adalci. Ko bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin zaben adalci basu dubawa."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng