Shugabannin kudancin Kaduna sun nemi na basu kudi kafin a samu zaman lafiya - El-Rufa'i

Shugabannin kudancin Kaduna sun nemi na basu kudi kafin a samu zaman lafiya - El-Rufa'i

Nasir El-Rufa'i, gwamnan jihar Kaduna, ya ce gwamnotocin jihar na baya su kan biya wasu shugabanni a kudancin jihar Kaduna da ake zargin suna rura wutar kashe-kashe a yankin.

El-Rufa'i ya bayyana cewa ba zai biya bukatar 'yan ta'adda ta hanyar basu kudi ba, sai dai ya tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka samu hannunsa a cikin kashe-kashen jama'a a kudancin Kaduna.

Da ya ke magana a wani shirin gidan talabijin na 'Channels', gwamnan ya bayyana cewa gwamnatocin baya na bawa shugabannin yankin kunshin kudi domin kar a samu barkewar rikici.

Duk da yawan jami'an tsaro da gwamnati ta tura zuwa kudancin jihar Kaduna, har yanzu ana cigaba da samun rahoton kai hare-hare masu nasaba da kabilancin a yankin.

Wasu sun zargi gwamna El-Rufa'i da nuna bangaranci da halin 'ko in kula' a kan halin rashin tsaro da kudancin Kaduna ke ciki.

Amma yayin da ya ke magana a shirin gidan talabijin din Channels, El-Rufa'i ya ce wasu daga cikin shugabannin yankin su na jin haushinsa saboda ya dakatar da biyansu wadancan kudade da su ka saba karba.

"Ma su irin wadannan maganganu basu da wata hanyar samun kudi sai daga aljihun gwamnati. Gwamnatocin baya da su ka gabata suna biyansu wasu kudi duk wata da sunan kudin tsaro. Mun dakatar da biyan wadannan kudade, saboda wannan dalili ne suke cewa na dauki bangare," a cewarsa.

Shugabannin kudancin Kaduna sun nemi na basu kudi kafin a samu zaman lafiya - El-Rufa'i
El-Rufa'i
Asali: Facebook

Sannan ya cigaba da cewa; "ina jin duk abubuwan da su ke fada a kaina. Nine gwamnan jiha, idan basu zageni ba, wa zasu zaga?, musamman gwamna irina da ya ki amincewa da biyansu kudi don kar su tashi hankalin jama'a.

"Sun saba da yadda gwamnatocin baya ke lallabasu, su kirasu, su ci abinci, su sha shayi tare da gwamna, sannan a dauki kunshin kudi a basu. Haka ake tafiya a shekaru 20 da suka gabata.

"Mun yi watsi da wannan tsari bayan hawanmu gwamnati, kuma babu wani wanda zai gana da gwamna ko ya ziyarci gidan gwamnati matukar ba da niyyar kulla sulhu ko tattauna zaman lafiya ya zo ba. Bani da lokacinsu.

DUBA WANNAN: Babu ruwan Buhari: Masari ya fadi ma su laifi a matsalar rashin tsaro a Katsina

"Bani da lokacin sauraron shirme, ba kuma zan biya bukatunsu ba. Ba zan biya bukatun mutanen da basu iya komai ba sai tayar da hankalin mutane ta hanyar shirya kashe-kashen jama'a.

"Ta haka su ke samun kudi ya shiga asusunsu na banki tare da samun tallafin kudade daga kasashen ketare. Sun fi son hakan a kan a samu zaman lafiya mai dorewa a yankin."

Gwamnan ya kara da cewa zai cigaba da aiki da jami'an tsaro wajen zakulo da shugabannin yankin da rahoton bincike ya nuna cewa akwai hannunsu a cikin tashe-tashen hankula da kisan jama'a a kudancin jihar Kaduna.

A cewar gwamnan, gwamnatinsa za ta gurfanar da irin wadannan shugabanni da zarar an kammala tattara isassun hujjoji a kansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel