CAN ta fadawa Kungiyar Shari’a kashe Janar Lekwot ba zai kawo zaman lafiya ba
Manjo Janar Zamani Lekwot ya maida martani ga kiran da wasu malaman addinin musulunci su ke yi na cewa a zartar da hukuncin kisan-kan da aka taba yi masa.
Janar Zamani Lekwot da CAN sun yi magana da jaridar Vanguard a jiya, su na cewa kashe shi kamar yadda wasu su ke bukata, ba zai kawo zaman lafiya a jihar Kaduna ba.
Tsohon sojan ya yi wannan magana ne bayan shugabannin kungiyar CAN sun kai masa ziyara. Lekwot ya yi mamakin yadda wasu ke kyankyasa kwan kiyayya a yankin.
“Abin da Najeriya ta ke bukata a wannan lokaci shi ne hakuri da juna ba tare da lura da banbancin addini ko kabilanci ba, ba wai kiyayya ba.” Inji tsohon gwamnan sojin.
A game da maganar zartar masa da hukuncin kisa, Lekwot ya ce: “Babu abin da zan ce, raina kamar na kowa, ya na hannun Ubangiji, ba a hannun masu surutu ba.”
KU KARANTA: Kungiya ta ba Gwamnati shawarar kashe wasu manya 17 a Kudancin Kaduna
Lekwot ya roki Ubangiji ya tona asirin masharrantan da su ke kokarin cusa kiyayya a zukatan al’umma, a cewarsa wannan shiri da ake yi a Kaduna ba zai kai ko ina ba.
Da aka tambayi Lekwot ko ya na tsoron mutuwa, sai Janar din ya bada amsa da cewa: “Tsoro?” Ni tsohon Soja ne wanda aka yi wa horon jagorantar dakaru.”
Janar Lekwot ya yi tir da kashe-kashen Zango-Kataf, amma ya ce abin da ya kawo rikicin shi ne yunkurin sake wurin da kasuwar garin ta ke, wanda jama’a ba su so.
“Ta ina maganar komawa lamarin nan ya zama maganin kawo karshen kashe-kashen Kudancin Kaduna. Abin da ke faruwa a Kaduna, kusan ya na faruwa a ko ina.”
Bayan haka mun ji cewa shugaban CAN, Dr. Supo Ayokunle, ya isa Kaduna, ya soki kiran majalisar shari’a, kuma ya ce zai gana da gwamna Nasir El-Rufai a yau.
Supo Ayokunle ya ce kashe-kashen da ake yi a yankin ya jawowa jihar bakin-suna, ya ce dole wannan ta’adi da ake yi da ma wasu bangarorin kasar ya tsaya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng