Jami’an Hukumar kwastam sun yi dacen tare kayan N10b a Garin Ibadan

Jami’an Hukumar kwastam sun yi dacen tare kayan N10b a Garin Ibadan

A ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta, 2020, dakarun hukumar kwastam na reshen Legas, su ka bada sanarwar yin wani babban kame a Najeriya.

Hukumar hana fasa kaurin ta bakin babban jami’inta, Usman Yahaya, ta ce ta yi ram da wasu haramtattun kayan da darajarsu su ka haura Naira biliyan.

Usman Yahaya ya yi wannan jawabi ne a karshen makon jiya a Legas. Ya ce sun cafke wadannan kaya ne a iyakar a garin Ido, da ke Ibadan, jihar Oyo.

Kamar yadda jami’in hukumar na reshen Legas ya shaidawa Manema labarai, wadannan kaya sun biyo ta kan titin Eruwa ne a yankin Ido.

Mai magana da yawun bakin hukumar, Peter Duniya, ya sa hannu a wannan jawabi. Ya ce kayan da su ka karbe sun hada motoci 34 da gwanjon tufafi.

Haka zalika jami’an na kwastam masu yaki da fasa kauri sun yi ram da shinkafa da tabar wiwi.

KU KARANTA: An gano wani Bawan Allah da aka tsare na shekara 15 a Kano

Jami’an Hukumar kwastam sun yi dacen tare kayan N10b a Garin Ibadan
Shugaban Hukumar kwastam, Hameed Ali
Asali: Depositphotos

“Wasu masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa sun ga iyakarsu a lokacin da jami’an su ka yi ram da su a garin Ido, Ibadan, a jihar Oyo bayan samun kishin-kishin.”

Jawabin hukumar ya ce: “Kayan da aka karbe sun hada da sababbi da gwanjon motoci 34 cike da kayan da aka hana shigowa da su irinsu tufafi, shinkafa da wiwi.”

“Duk da masu fasa kaurin sun yi yunkurin nuna taurin-kai da hadin-kan wasu ‘yan iskan gari, dakarun kwastam sun nuna kwarewar aiki, sun tare wadannan kaya.”

Kwastam ta ce ba a ji wa jami’in ta ko guda rauni ba wajen wannan aiki. Yanzu haka kayan su na tsare a babban dakin ajiyan hukumar da ke jihar Legas.

Yahaya ya ja-kunnen masu wannan danyen aiki su guji abin da zai kawowa shirin gwamnati cikas wajen samar da isasshen abinci, tare da neman hadin-kan jama'a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel