Buhari ya aika sakon gaisuwa ga Babangida yayinda ya cika shekaru 79 a duniya
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun sauran ‘yan Najeriya waje taya Ibrahim Babangida wanda ya cika shekaru 79 murna
- A wani sakon taya murna, Buhari ya ce za a dunga tuna aikin a Babangida ya yi wa Najeriya a koda yaushe
- Shugaban kasar ya yi adu’an Allah ya kara wa tsohon Shugaban kasar lafiya da nisan kwana
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta, ya bi sahun ‘yan Najeriya wajen taya tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Babangida, wanda ya cika shekaru 79 a duniya murna.
A wani sakon taya murna da kakakinsa, Femi Adesina ya saki, Buhari ya bayyana cewa a kullun ‘yan Najeriya za su dunga tuna kyawawan ayyukan Babangida.

Asali: UGC
Sakon ya zo kamar haka: “Yayinda tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya kara sabon shekara, Shugaban kasar ya yi amanna cewa kasar za ta dunga tunawa da ayyukansa a koda yaushe.
“Shugaba Buhari na addu’a ga Allah a kan ya ci gaba da kara wa Janar Babangida karfi, ya kara masa lafiya da tsawon rai."
An haifi tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Babangida a ranar 17 ga watan Agusta, 1941 sannan ya yi shugabanci tsakanin 1985 da 1993.
Tsohon janar din mai ritaya ya yi aiki a matsayin Shugaban rundunar sojin kasar kafin ya zama Shugaban kasa daga Janairun 1984 zuwa Agustan 1985.
KU KARANTA KUMA: Mazauna Abuja sun koka a kan yawan sace-sacen mutane
Wikipedia ta ruwaito cewa Babangida ya rike mukamai a rundunar soji sannan ya yi yaki a lokacin yakin basasan Najeriya.
Babangida wanda ya kasancce haifafan Minna, jihar Neja ya shiga rundunar sojin Najeriya a ranar 10 ga watan Disamba, 1962, bayan ya halarci makarantar kwalejin horon soji, wanda ke Kaduna.
A wani labari na daban, IBB ya yi martani a kan rahoton da ake yadawa wanda ke ikirarin cewa yana neman matar aure.
A yayin da aka tambayesa a wata tattaunawa da aka yi da shi idan da gaske ne yana neman matar aure, tsohon shugaban kasar ya ce: "hakan kafafen yada labarai ke so. Mutane da dama suna tambayata gaskiyar lamarin."
Tun bayan rasuwar Maryam Babangida a 2009, tsohon shugaban kasar bai sake yin aure ba sai dai zama da yake yi da 'ya'yansa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng