Dole a hukunta Lekwot da sauransu saboda rigimar shekarar 1992 na Zangon-Kataf

Dole a hukunta Lekwot da sauransu saboda rigimar shekarar 1992 na Zangon-Kataf

- Wata majalisa ta Shari’a ta yi magana game da rigimar Kudancin Kaduna

- Kungiyar addinin ta ce dole a hallaka wasu domin a zauna lafiya a yankin

- SCSN ta na so a hukunta duk wadanda aka kama da laifin tada rikicin 1992

Majalisar Shari’a ta SCSN ta ce gazawar gwamnatin tarayya na hukunta wadanda su ka kawo tarzoma a garin Zangon-Kataf ne abin da ya sababba rikicin jihar Kaduna.

SCSC ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta yankewa mutanen da aka samu da hannu a laifin rikicin Zangon-Kataf shekaru 28 da su ka wuce hukuncin da ke kansu na kisan-kai.

Sakataren SCSC, AbdurRahman Hassan, ya yi jawabi gaban manema labarai a ranar 13 ga watan Agusta, ya ce dole a koma a duba abin da ya auku a lokacin gwamnatin soja.

An samu wasu manya da laifin tada tarzoma a garin Zangon-Kataf, a kudancin jihar Kaduna, amma shugaban kasa a wancan lokaci, Janar Sani Abacha ya yi masu afuwa.

KU KARANTA: Malamai su ke hura wutan rikicin Kaduna - Gwamna El-Rufai

Dole a hukunta Lekwot da sauransu saboda rigimar shekarar 1992 na Zangon-Kataf
Gwamnatin Abacha ce ta yi wa Lekwot afuwa
Asali: Getty Images

Wannan kungiya ta addini ta na so gwamnati ta duba wannan hukunci da aka yi, ta kuma dabbaka shi. A cewarta, ta hakan ne za a samu zaman lafiya a kasar nan.

“Mu na so a hallaka wadanda aka yi wa afuwa game da rikicin Zangon-Kataf, domin ta haka ne kurum za a samu zaman lafiya a yankin.” Inji Malam AbdurRahman Hassan.

A watan Mayun 1992 aka kaure da mummunan tashin-tashina tsakanin Musulmai da Kiristoci a Kaduna. Wadannan rikici ya ci Hausa da Katafawan da ke zaune a Zangon-Kataf.

Sakamakon kashe-kashe da asarar dukiyar da aka yi a karamar hukumar Zangon-Kataf, Ibrahim Badamasi Babangida ya kafa kwamiti na musamman domin ya binciki rigimar.

Wannan kwamiti ya samu Janar Zamani Lekwot mai ritaya da wasu mutane 16 da laifi, ya kuma yanke masu hukunci kisa, amma a karshe Sani Abacha ya yi masu afuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel