KDMDC: Gwamnatin Kaduna ta bude kasuwar Abubakar Gumi daga yau

KDMDC: Gwamnatin Kaduna ta bude kasuwar Abubakar Gumi daga yau

Bayan tsawon lokaci, gwamnatin jihar Kaduna ta bude babban kasuwan nan na Sheikh Abubakar Gumi da ke garin Kaduna.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta bada iznin a koma wannan kasuwa ne a ranar Juma’a, 14 ga watan Agusta, 2020.

Wannan sanarwa ta bude kasuwar Abubakar Gumi ta fito daga bakin kamfanin kamfanin da ke kula da cigaban kasuwani a jihar Kaduna watau KMDMC.

Kamar yadda shugaban hukumar kasuwanni na Kaduna, Hafiz Bayero ya bayyana a cikin makon nan, za a fara bude kasuwannin ne da na Sheikh Abubakar Gumi.

KMDMC ta tanadi takunkumin rufe fuska 10, 000 da fanfo 20 da aka kafa. Bayan haka kamfanin ya saye na’urorin auna dumin jiki da kuma man goge hannuwa.

A sanarwar da aka bada, za a rika ciniki ne tsakanin karfe 9:30 na safe zuwa 4:30 na kowace rana. Bayan an tashi kasuwa ba a halattawa kowa cigaba da saida kaya ba.

KU KARANTA: Kasar waje ta gargadi mutane game da shiga Kaduna da wasu jihohi

Gwamnatin Kaduna ta bude kasuwar Abubakar Gumi a yau - KDMDC
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai Hoto: Twitter
Asali: Facebook

Duk wanda aka kama ya na saida kaya bayan wannan lokaci zai rasa dukiyarsa har abada.

Gwamnati ta bada shawara ga mutane da ‘yan kasuwa su rika zuwa kasuwar a motocin haya saboda tsaurara matakai da za ayi na ajiye motoci da kuma gine-gine da ake yi a yankin.

A cewar KMDMC, za a rika sauke kaya kawai ne bayan an tashi kasuwa. Gwamnati ta bukaci jama’a su rika rufe fuskokinsu a ko yaushe, sannan su gujewa shiga ciinkoso.

Bayan ganin yadda abubuwa su ke wakana, ana sa rai za a bada iznin cigaba da mu’amalar kasuwanci a sauran wurare da ke fadin jihar kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Gwamnati ta rufe kasuwanni da makarantu ne a watan Maris bayan barkewar cutar COVID-19. An yi wannan ne domin kare rayukan al’umma da ke jihar Kaduna.

Mataimakiyar gwamnan Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe, ta ce za a rufe duk wata kasuwa da aka samu ta na sabawa sharudan COVID-19 da aka sa daga baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel