Akwai yiwuwar Najeriya ta burma cikin wani sabon matsin tattalin arziki - Agba

Akwai yiwuwar Najeriya ta burma cikin wani sabon matsin tattalin arziki - Agba

Najeriya ta na fuskantar barazanar sake komawa cikin matsin lambar tattalin arziki muddin motsawar tattalin kasar bai zabura a karshen shekarar nan ba.

Jaridar The Nation ta ce gwamnatin tarayya ta bada wannan gargadi, ta ce ta hararo dakushewar tattali. Gwamnati ta yi wannan bayani ne a ranae 13 ga watan Agusta, 2020.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta na fuskantar kalubale wajen samun kudin shiga, wanda hakan zai jefa kasar cikin matsalar gaza biyan bashi idan ba a magance matsalar ba.

Karamin ministan kudi, da kasafin tattalin arziki, Clement Agba, ya bayyana wannan a lokacin da ya zauna da kwamitocin tattalin arziki da bashi na majalisar wakilai.

Clement Agba ya halarci wannan zama ne a madadin babbar minista, Zainab Ahmed, inda ya shaidawa ‘yan majalisar hadarin da tattalin arzikin kasa ya ke fuskanta.

Agba ya ce Najeriya ta yi fama da matsin tattali a farkon shekarar nan a dalilin annobar COVID-19. Wannan annoba ta jawo karyewar farashin gangar mai a Duniya.

KU KARANTA: N4tr sun yi dabo daga asusun rarar mai a CBN wajen aikin NIPPs – Majalisa

Akwai yiwuwar Najeriya ta burma cikin wani sabon matsin tattalin arziki - Agba
Ministan kasafin tattali da kudi, Clement Agba
Asali: Twitter

Ministan ya ke cewa saukar farashin mai ya jawowa gwamnati asarar kusan 65% na kudin shiga a shekarar nan, wanda wannan ya na da tasiri wajen shigowar kudin kasar waje.

Karamin ministan kudin ya ce gwamnati ta daidaita farashin Dalar Amurka daga N360 zuwa N379 saboda wannan matsala ta rashin samun isasshen kudin kasar waje.

Daga cikin cikas da gwamnatin tarayya ta samu a sanadiyyar annobar COVID-19, akwai karancin haraji da ake karba na shigo da kaya saboda rufe iyakokin kasashe da aka yi.

Haka zalika annobar ta taba harajin VAT da kudin hatimi. Hatta harajin da ake karba daga hannun kamfanoni ya yi kasa don haka gwamnati ta rage buri a sabon kasafin 2020.

Mista Agba ya ce karfin kudin mai ya na da tasiri kan jimillar tattalin arzikin kasa na GDP. A cewar ministan, Najeriya ta rage adadin man da ta ke hakowa saboda matakin OPEC.

Game da tashin farashin kaya, Agba ya ce alkaluma za su takaita yadda su ke na tsawon lokaci. Ana sa ran kasafin 2021 da MTEF/FSP na 2023 su taimakawa tattalin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng