Gwamnatin Najeriya ta roki kasashen Duniya su taimaka mata da kayan yaki
Gwamatin tarayya ta yi kira da babbar murya ga kasashen da ake ji da su a Duniya da su yi watsi da surutan masu surutu, su taimakawa Najeriya da makamai.
Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto ministan al’adu da yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya na rokon kasashe su tallafawa gwamnatin Najeriya da kayan yaki.
Ministan ya yi wannan roko a madadin gwamnatin Buhari ne a lokacin da ya bayyana a gaban NAN a yau, 13 ga watan Agusta, 2020, a babbn birnin tarayya Abuja.
Lai ya ce: “Ina so in yi amfani da wanan dama in ce kasashen ketare za su iya taimaka mana fiye da abin da su ke yi a halin yanzu.”
“Wajen yakar ‘yan ta’adda, mu na bukatar kayan aiki da makamai.”
“Lokacin da kasashen waje su ka biyewa rade-radi marasa tushe wajen hana kasar mu kayan da ake bukata da makamai wajen yaki da rashin tsaro, ba ka isa ka juya ka zargi kasar da rashin yakar ta'addanci ba."
KU KARANTA: Buhari ya taso manyan sojoji a gaba a kan harkar rashin tsaro
A cewar ministan yada labaran, ‘wasu manyan Duniya sun ki saidawa kasar muhimman makaman da ta ke bukata.'
“Fiye da shekaru biyu ko uku kenan yanzu, mun biya kudin muhimman makamai amma ba a kawo mana su ba, sun kuma ki saida mana bangarorin kayan aiki.”
Lai Mohammed ya kara da cewa: “Ina tunani rokonmu gare su shi ne, su agazawa Najeriya da kaya masu amfani domin mu yaki rashin tsaro da kyau.”
Wajen auna kokarin gwamnatin nan, Lai ya bukaci mutane su rika la’akari da yadda gwamnatin APC ta tsinci kasa a 2015, da kuma halin da ake ciki yanzu.
Bayan haka, Ministan ya ce: “Mu na yaki da miyagun mutane, ko a Arewa moas gabas, ko a Arewwa maso yamma. Wadannan miyagu su na da masu taimaka masu.
Yakin sunkuru Najeriya ta ke yi a yau inji Ministan. Ya ce: “Mutane su fahimci cewa yau an maida lamarin addini da kabila abin fada.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng