WAEC: Ganduje ya yi afuwa ga daliban kwaleji da suka yi mishi zanga-zanga
- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin gafara ga dukkan daliban da suka shiga zanga-zangar da aka yi a kwalejin kimiyya na Dawakin Tofa da ke jihar Kano
- Ganduje ya yi masu afuwan ne domin yan aji shida su samu damar zana jarrabawar WAEC
- Gwamnan ya kara da jan kunnen daliban da su kasance masu bin doka don tabbatar da cewa irin wannan lamarin bai sake faruwa ba a makarantar duk rintsi
Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin gafara ga dukkan daliban da suka shiga zanga-zangar da aka yi a kwalejin kimiyya na Dawakin Tofa da ke jihar Kano.
A wata takardar da Lauratu Ado Diso, babbar sakatariyar ma'aikatar ilimi ta jihar Kano ta sa hannu a ranar Alhamis, ta ce Gwamnan ya bai wa ma'aikatar ilimi ta jihar umarnin.
Ya ce a dawo da daliban aji shida na makarantar domin su rubuta jarabawar kammala sakandire, jaridar Sun ta ruwaito.
Wannan takardar ta fita ne dauke da kwanan wata 12 ga watan Augustan 2020, bayan an mika takardar ga kwamishinan ilimi na jihar, Muhammadu Sanusi S. Kiru, kafin a fara taron majalisar zartarwa ta jihar.
A takardar, gwamnan ya kara da jan kunnen daliban da su kasance masu bin doka don tabbatar da cewa irin wannan lamarin bai sake faruwa ba a makarantar duk rintsi.
An shawarci iyayen da suka biya wa yaran kudin jarabawar a makarantar da su gaggauta dawo da yaran kwalejin don fara shirin jarabawar, wacce za a fada a ranar 17 ga watan Augustan 2020.
KU KARANTA KUMA: Lukman ya fallasa wani sirri da zagon kasa a jam'iyyar APC
Wani mahaifi na daya daga cikin daliban, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya nuna farin cikinsa yayin da ya tabbatar da cewa 'ya'yansu sun koyi darasi daga kuskurensu.
A gefe guda, hukumar shirya jarrabawar makarantun sakadandare ta Najeriya, NECO, ta fitar da jadawalin jarrabawar shekarar 2020 da ka'idojin rubuta jarrabawar ta bana.
Hakan na zuwa ne a lokacin da hukumar jarrabawar ta bayyana cewa za ta saka naurar daukan bidiyon sirri na CCTV a dakunan rubuta jarrabawar domin hana magudi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng