NGF: Jihohi su na neman kudin magance matsalar tsaro wajen Gwamnatin Buhari

NGF: Jihohi su na neman kudin magance matsalar tsaro wajen Gwamnatin Buhari

Kungiyar NGF ta gwamnonin jihohin Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimaka mata da aron kudi domin shawo kan matsalar rashin tsaro.

A ranar Talata, 11 ga watan Agusta, 2020, NGF ta nemi tallafin gwamnatin tarayya a dalilin kudin da su ke kashewa daga asusun jihohinsu a kan sojoji da sauran jami’an tsaro.

Jaridar Daily Trust ta ce wannan ce matsayar da aka dauka bayan ganawar gwamnoni da shugaban kasa a karkashin shugaban NGF, Kayode Fayemi da Babagana Zulum.

An yi wannan zama ne a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja ta kafafen zamani. An samu gwamna guda da ya wakilci kowane bangare na fadin Najeriya.

Sauran wadanda su ka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, hafsun sojoji da shugabannin hukumomin tsaro da kwamitin tsaro na NGF.

A wannan taro, gwamnoni sun shaidawa shugaban kasa da majalisar cewa matsalar da su ke fuskanta na rashin aikin yi da talauci ne su ke taimakawa wajen tabarbarewar tsaro.

KU KARANTA: Gwamnan Legas zai jagoranci yakin neman zaben APC a Ondo

NGF: Jihohi su na neman kudin magance matsalar tsaro wajen Gwamnatin Buhari
Shugaban kasa Buhari a taro
Asali: Facebook

Gwamnonin sun kuma alakanta matsalar da rashin yarda da ke tsakanin al’umma da jami’an tsaro da kuma barkowar makamai, game da rashin hadin-kai tsakanin hafsun sojoji.

Haka zalika gwamnonin sun tunawa shugaban kasa da gudumuwarsu, musamman na bada damar a zari Dala biliyan daya daga asusun rarar mai domin a saye kayan yaki.

Wakilan gwamnonin sun roki shugaban kasa ya taimakawa jihohi da aron kudi domin su shawo kan matsalar da su ke fama da ita, amma shugaban kasar bai ce komai ba game da wannan.

Da aka tuntubi mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya tabbatar da cewa Farfesa Ibrahim Gambari ya ji bukatar gwamnonin, kuma za a zauna a duba lamarin.

Kungiyar CHRICED a karkashin Dr. Zikirullahi M. Ibrahim, ta ce wannan dabara ce ta gwamnoni na wawurar kudin kamar yadda wasu su ka yi da aka ba su kudi su biya albashi.

Ita ma kungiyar CISLAC ta na ganin aron kudin ba zai kawo karshen matsalar tsaro a jihohi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng