Shehu Sani ya fada wa Buhari abubuwa 3 da zai yi domin shawo kan rikicin kudancin Kaduna

Shehu Sani ya fada wa Buhari abubuwa 3 da zai yi domin shawo kan rikicin kudancin Kaduna

- Shehu Sani ya ce tattaunawa da shugabannin kudancin Kaduna zai taimaka wajen kawo karshen kashe-kashe a yankin

- Tsohon Sanata ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gayyaci dattawan da shugabannin yankin don tattaunawa

- Tun farko, Sani ya bayyana cewa a yanzu sarakunan gargajiya ne aka fi kashewa tare da garkuwa da su

Shehu Sani ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saurari shugabannin kudancin Kaduna, ganin cewa zubar da jinin da ake yi ya ki cinyewa a yankin.

Tsohon dan majalisar, wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Augusta, a yayin da lamurran 'yan bindiga ke sake tsamari a yankin Kaduna ta kudun.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Sani ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai iya gano gaskiyar lamari da kuma musababbin fadan da ake yi a yankin.

Idan za a tuna, rikici a yankin ya kawo karshen rayukan daruruwan Mutane a yayin da ake ci gaba da kutsawa sauran yankunan.

Shehu Sani ya fada wa Buhari abubuwa 3 da zai yi domin shawo kan rikicin kudancin Kaduna
Shehu Sani ya fada wa Buhari abubuwa 3 da zai yi domin shawo kan rikicin kudancin Kaduna Hoto: Koko TV
Asali: UGC

A ranar Litinin, 10 ga watan Augusta, shugaban kasa Buhari ya yi taro da gwamnonin arewa maso gabas a Abuja.

Gwamnonin da suka samu halartar taron sun hada da Umaru Fintiri na jihar Adamawa, Bala Mohammed na jihar Bauchi, Farfesa Babagana Zulum na Borno, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, Darius Ishaku na jihar Taraba da Mai Mala Buni na jihar Yobe.

An yi taron ne bayan kwanaki kadan da shugaban kasa ya bada umarnin sake tsari da gyaran yanayin tsaro na kasar nan.

Shehu Sani ya ce, hanya daya ta maganin 'yan bindiga shine idan shugaba Buhari ya gayyaci shugabannin yankin don jin ta bakinsu.

KU KARANTA KUMA: Muna roƙon 'yan Najeriya su ƙara haƙuri kan matsalar rashin tsaro - Buhari

“Idan har shugaban kasa na son sanin ainahin abunda ke faruwa a Kudancin Kaduna da kuma samo mafita mai dorewa kan rikici da zubar a wajen, dole ya gayyaci shugabanni da dattawan kudancin Kaduna, ya sauraresu sannan ya tattauna dasu kai tsaye,” in ji tsohon dan majalisar.”

Tun farko dai Sani ya bayyana cewa a yanzu sarakunan gargajiya ne aka fi kashewa tare da garkuwa da su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel