Saudiyya: Wani bawan Allah zai kai matarsa kotu don ta yi masa leken asiri a WhatsApp
- Wani magidanci a kasar Saudiyya na shirin kai matarsa kotu don ta yi masa leken asiri a WhatsApp
- Ya ce ta shafe tsawon wata tara tana kutse a WhatsApp dinsa sannan tana ganin dukkan sakonni da bidiyo da aka turo masa babu saninsa
- A bangaren matar kuwa, ta bukaci ya sauwake mata igiyoyin aurensa da ke kanta kuma ya gayyaci kudin tallafin da zai hada mata da takardarta
Wani bawan Allah a kasar Saudiyya na yunkurin kai matarsa gaban kuliya a kan leken asirin da take masa a kan sakwanninsa na manhajar WhatsApp na tsawon wata tara.
Kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta wallafa, mutumin ya gane cewa matarsa wacce malamar makaranta ce, tana kutse a WhatsApp dinsa sannan tana ganin dukkan sakonni da bidiyo da aka turo masa babu saninsa.

Asali: UGC
Kamar yadda yace, abin da matarsa ta aikata masa laifi ne babba kuma zamba ne na yanar gizo.
A bangaren matar kuwa, ta bukaci ya sauwake mata igiyoyin aurensa da ke kanta kuma ya gayyaci kudin tallafin da zai hada mata da takardarta.
A yayin da aka tuntubi mata, ba tace komai a kan batun ba. Sai dai ta tabbatar da cewa ta nemi a raba auren saboda bata son bayyana sirrin aurensu ga jama'a.
KU KARANTA KUMA: Gwarzo: Wani matashi ya aura mata biyu a lokaci daya kuma rana daya (Hotuna)
A wani bangare kuwa, wata kwararriya a harkar tsaron yanar gizo ta yi gargadi a kan amfani da Wi-Fi na kyauta da ake samu a filayen jiragen sama da otel.
Ta ce za a iya yi wa mutum kutsen sirri a hakan.
A wani labari na daban, wata Baiwar Allah da ke yankin Embakasi ta rabu da mijinta bayan tsawon shekaru su na zaman aure a sakamakon kama shi da ta yi da laifin yaudara.
Shamin ta shafe shekaru kimanin goma tare da maigidanta, ta na zaton ya na aiki ne a babban filin tashi da saukar jiragen sama na Jomo Kenyatta a kasar Kenya.
A wata hira da ta yi da Anthony Ndiema a filin Nisamehe a wata tashar talabijin a kasar Kenya, Shamim ta ce sai daga baya ta samu labarin inda mijinta ya ke aiki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng