Messi bai yi atisaye ba yayin da Barcelona ke shirin haduwa da Bayern Munchen

Messi bai yi atisaye ba yayin da Barcelona ke shirin haduwa da Bayern Munchen

- Tauraron ‘Dan wasa Lionel Messi bai iya halartar wani atisayen Barcelona ba

- Kungiyar Bayern Munich za ta yi murnar Messi ya ki buga wasan da za su yi

- Mai horas da kungiyar Barcelona, ya ce babu abin damuwa game da lamarin

Kungiyar Barcelona ta na neman shiga matsala a gasar zakarun Nahiyar Turai a sakamakon halin da shararren ‘dan wasanta Lionel Messi ya shiga.

Lionel Messi bai iya halartar atisayen da ragowar ‘yan Barcelona ba. Hakan ya faru ne a sanadiyyar buguwar da ‘dan wasan gaban ya yi a karawar Napoli.

Rahotanni daga gidan rediyon Sifen, Cope sun ce ‘dan wasan mai shekara 33 bai iya tabuka komai a ranar Lahadi bayan an dawo bakin aiki a filin Camp Nou.

Akwai yiwuwar har yau Messi bai fita aiki ba kamar yadda Cope ta bayyana. ‘Dan kasar Argentinan ya na ta dingishi bayan karo da ya yi da Kalidou Koulibaly.

Messi ya zauna da likitoci ne a karshe makon jiya, sannan ya yi aiki shi kadai a dakin atisaye ba tare da ya shiga cikin fili tare da sauran tawagar ‘yan wasa ba.

KU KARANTA: Ana rade-radin Messi zai bar Barcelona

Messi bai yi atisaye ba yayin da Barcelona ke shirin haduwa da Bayern Munchen
Messi zai hadu da Bayern Munchen
Asali: Getty Images

A wani rahoton, ko a jiya da ake hutu, ‘dan wasan ya fita aiki, ya na cigaba da kokarin shawo kan buguwar da ya yi a gwiwa da nufin iya buga muhimmin wasan da za su yi.

Idan ta tabbata ‘dan kwallon ba zai samu damar buga wasansu da Bayern Munich ba, wannan zai zama labari maras dadi ga duk magoya bayan kungiyar ta Sifen.

A shekarar nan, Barcelona ta dogara kan gwarzon ‘dan wasan Duniyan, musamman bayan Luis Suarez ya kwanta jinya. Tun 2015 rabon kungiyar da lashe kofin gasar Turan.

Ita kuma kungiyar Bayern Munich wanda za ta fafata da Barcelona a zagaye na gaba na gasar Turai a ranar Juma’ar nan mai zuwa, za ta ji dadin wannan labari.

Kocin Barcelona Quique Setien, ya ce Messi ya bugu, amma ba ya tunanin wannan zai hana shi buga wasa. Ya ce: “Za mu duba lamarin, ba zai zama matsala ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel