Laifin manyan kasa ne da aka saba doka a gangamin APC, jana’izar Kashamu - inji PTF

Laifin manyan kasa ne da aka saba doka a gangamin APC, jana’izar Kashamu - inji PTF

Kwamitin shugaban kasa na yaki da annobar COVID-19 a Najeriya ta zargi gwamnonin jihohi, sarakunan gargajiya da malaman addini da jawo cincirindo.

PTF ta ce laifin manyan kasar ne ya jawo mutane su ka rika yin cinkoso wajen gangamin yakin neman zaben gwama a jihar Edo, da kuma jana’izar Buruji Kashamu a Ogun.

A ranar 10 ga watan Agusta, kwamitin PTF ya zanta da manema labarai kamar yadda ya saba lokaci bayan lokaci, kwamitin ya yi takaicin abubuwan da su ka faru kwanan nan.

Sanata Buruji Kashamu ya mutu ne bayan ya yi fama da COVID-19. An bizne shi a Ijebu, Ogun, inda mutane rututu su ka sabawa sharudan da PTF ta gindaya na gujewa COVID-19.

Jam’iyyun APC da PDP sun shirya gangami na yakin neman zaben gwamnan Edo. A nan ma dinbin mutane sun samu halarta ba tare da da yawa sun rufe fuskokinsu da takunkumi ba.

Da aka tambayi shugaban PTF, Dr. Sani Aliyu, game da lamarin, ya ce: “Dole in ce mun damu da yanayin yadda ake sabawa ka’idoji a wurin irin wadannan taro.”

KU KARANTA: An samu karin mutane 200 masu COVID-19 a ranar Litinin

Laifin manyan kasa ne da aka saba doka a gangamin APC, jana’izar Kashamu - inji PTF
Shugaban kwamitin PTF, Sani Aliyu
Asali: Twitter

“Maganar ita ce, mun san cewa COVID-19 ba kamar sauran annoba ta ke ba. Idan da cutar Ebola mu ke fama da ita, da yanzu gawawwaki sun cika titi, mutane su na nishi.”

Sani Aliyu ya ce cutar COVID-19 ta kan yi wa Bayin Allah kisan mummuke ne. A cewarsa, a wannan lokaci babu bukatar a cigaba da kira ga jama’a su kare kansu da kansu.

“Mu na fama ne da annobar da babu mai iya ganinta.”

Dr. Aliyu ya ke cewa dole shugabanni a kowane mataki su bi matakan da aka bayyana domin ana fama da annobar da mafi yawan jama’a ba za su san da wadanda su ke hulda ba.

A game da lamarin rufe fuskoki, Aliyu ya ce yin hakan taimakon kai ne kuma damuwa da lafiyar sauran mutane ta yadda mutum ba zai dauki cutar ba, kuma ba zai yada ta ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel