Tsohon Shugaban Alpha Beta ya nemi EFCC ta bibiyi takardun korafin da ya gabatar

Tsohon Shugaban Alpha Beta ya nemi EFCC ta bibiyi takardun korafin da ya gabatar

Wani tsohon shugaban kamfanin Alpha Beta Consulting Limited and Alpha Beta LLP, Mista Dapo Apara ya yi kira ga EFCC ta binciki zargin da ke kan wannan kamfani.

A 2018, Dapo Apara ya rubuta takarda zuwa ga hukumar EFCC ya na korafin cewa kamfanin Alpha Beta ya ki biyan kudin harajin da ke kansa na sama da Naira biliyan 100.

A wancan lokaci, Apara ya ce kamfanin sun gujewa biyan harajin ne saboda su na da daurin gindin ‘yan siyasa. Ana zargin Bola Tinubu ya na cikin masu wannan kamfani.

Ana ganin daga lokacin zuwa yanzu, hukumar ta ki maida hankali game da wannan korafi, ta ce ba a ba ta isassun hujjojin da za su taimaka mata wajen binciken wannan zargi ba.

Mista Apara ya yi magana da jaridar Punch a ranar Lahadi, ya na kira ga sabon mukaddashin shugaban EFCC, Umar Mohammed, ya sake duba wannan korafi da ya gabatar.

“Zan so sabon shugaban EFCC ya yi abin da ya kamata, ya bibiyi korafina. A shirye na ke a ko yaushe in gabatar da duk wasu karin hujjoji da ake bukata.” Inji Apara.

Tsohon Shugaban Alpha Beta ya nemi EFCC ta bibiyi takardun korafin da ya gabatar
Tsohon Shugaban Alpha Beta ya nemi EFCC ta bibiyi takardun korafin da ya gabatar
Asali: UGC

KU KARANTA: Atiku ya jefi Osinbajo da zargin awon gaba da Biliyoyin kudi

Tsohon shugaban kamfanin ya ce Alpha Beta mai tattara haraji a jihar Legas ta hada kai da wani kamfani mai suna Ocean Trust Limited wajen satar dukiyar gwamnati.

Ko da cewa duk rade-radin da ake yi, babu wata hujja da ke nuna Bola Tinubu ne ya mallaki Alpha Beta, akwai alamun cewa ba zai rasa alaka da Ocean Trust Limited ba.

Adireshin wannan kamfani na Ocean Trust Limited ya zo daidai da ainihin adireshin ofishin tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, wanda ake kira ‘Freedom House’.

Takardun da aka samu daga ma’aikatar CAC mai alhakin yi wa kamfanoni raijista ya nuna kamfaninsu Yemi Osinbajo na Simmons Coopers Partners sun taba aiki da Ocean Trust.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya musanya zargin cewa ya na da hannu wajen laifin aikata ba daidai ba. Osinbajo ya rab da kamfanin gabanin zaben 2015.

Bola Tinubu ne ya fara ba kamfanin Alpha Beta kwangilar karbar haraji a Legas, bisa shawarar kwamishinonin wancan lokaci; Yemi Osinbajo, Wale Edun, da Yemi Cordoso.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel