Sojoji sun kama manyan 'yan bindiga 8 a kudancin Kaduna

Sojoji sun kama manyan 'yan bindiga 8 a kudancin Kaduna

Dakarun rundunar sojin Najeriya da ke aiki a karkashin atisayen Ofireshon Safe Haven (OPSH) sun samu nasarar kama wasu manyan 'yan bindiga 8 da ke kai hare-hare a kudancin jihar Kaduna.

A cikin wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa, rundunar soji ta sanar da cewa wani dan bindiga guda daya ya mutu yayin musayar wuta da dakarun atisayen OPSH da ke aiki a jihar Filato da wani bangare na jihar Bauchi da Kaduna.

Mutane da dama rahotanni suka sanar da cewa an kashe sakamakon hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a sassan kudancin jihar Kaduna.

Yayin bajakolin 'yan bindigar, kwamandan runduna ta 7 da ke kudancin jihar Kaduna, Kanal David Nwakonobi, ya ce an kama ma su laifin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma gudanar da bincike ta karkashin kasa.

"Dakarunmu, bayan samun bayanan sirri da kuma gudanar da bincike cikin sirri, sun samu nasarar cafke wasu 'yan bindiga 6 a karamar hukumar Lere a ranar 5 ga watan Agusta.

"Kazalika, dakarun soji tare da hadin gwuiwar 'yan kungiyar sa-kai sun kama wasu 'yan bindiga guda biyu a Chawai, wani gari da ke kan iyakar Kauru da Zangon Kataf a jihar Kaduna," a cewarsa.

Sojoji sun kama manyan 'yan bindiga 8 a kudancin Kaduna
Sojoji sun kama manyan 'yan bindiga 8 a kudancin Kaduna
Asali: Twitter

A cewar kwamandan, daga cikin makaman da aka samu a hannun 'yan bindigar akwai; wasu manyan bindigu na gida guda biyu, kananan bindigu na gida guda biyu, babura guda biyu, alburusai da sauransu.

DUBA WANNAN: Batanci ga Annabi: Kotun Kano ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin mawaki

Kwamnadan ya bayyana sunayen 'yan bindigar da aka kama kamar haka; Said Abubakar, Ali Amadu, Bawa Idi, Umar Dikko, Garba Damina da kuma Muhammad Ibrahim.

Sauran biyun da aka kama a karamar hukumar Kaura da Zangon Kataf sune; Adamu Joseph da William Barnabas.

Kanal Nkwakonobi ya kara da cewa za a mika 'yan ta'addar hannun rundunar 'yan sanda da zarar rundunar soji ta kammala yi mu su tambayoyi.

A cewar Kanal Nwakonobi, rundunar atisayen OPSH za ta cigaba da aiki da 'yan kasa nagari domin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a sassan kudancin jihar Kaduna da kewaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng