Duk da yunkurin Sojojinmu, Boko Haram su na ta’asa a yankin Chadi – Idriss Deby

Duk da yunkurin Sojojinmu, Boko Haram su na ta’asa a yankin Chadi – Idriss Deby

Shugaban kasar Chad, Idriss Deby ya ce kungiyar Boko Haram za ta cigaba da zama barazana a yankin tafkin Chad, duk da hare-haren da sojojinsa su ka kai kwanaki.

A ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, 2020, Idriss Deby, ya yi magana game da ‘yan ta’addan. Shugaban ya ce za a dauki lokaci mai tsawo ba a ga karshen rikicin ta’ddancin ba.

“Za mu cigaba da samun wannan sha’anin Boko Haram na tsawon lokaci.” Deby ya fadawa gidan rediyon Faransa wannan a lokacin da aka yi hira da shi a karshen makon jiya.

Yankin tafkin Chadi mai tarin arziki da ‘yan ta’addan Boko Haram su ka fitina, ya kunshi bangarorin Najeriya da iyakokin makwabta: Chadi, Kamaru, da Jamhuriyyar Nijar.

A farkon shekarar bana, sojojin kasar Afrikan su ka kai wa Boko Haram wasu hare-hare da nufin ganin bayansu, amma duk da haka akwai sauran jan aiki a gaban jami’an tsaron.

Shugaba Idriss Deby ya kara da cewa: “Za a cigaba da samun kutsowarsu. Kungiyar za ta cigaba da yin munanan barna a yankin tafkin Chadi.”

KU KARANTA: Shugaban Boko Haram, Shekau ya sake fitowa a sabon bidiyo

Duk da yunkurin Sojoji, Boko Haram su na ta’asa a yankin Chadi – Idriss Deby
Shugaban Najeriya da Idriss Deby a Chadi
Asali: Depositphotos

Tun 2009 ‘yan Boko Haram su ka bayyana a Arewa maso yammacin Najeriya. Kawo yanzu ‘yan ta’addan sun kashe fiye da mutane 36, 000, kuma babu ranar karshen rikicin.

Wannan lamarin rashin ratso ya kai zuwa kasashen Nijar, Kamaru, da Chadi da ke iyaka da Najeriya.

A watan Maris, kasar Chadi ta rasa sojojinta 98 a hannn mayakan kungiyar Boko Haram bayan an kai masu wani samame a garin Bohoma da ke kan gabar tafkin Chadi.

Ganin wannan gagarumar asara da Chad ba ta taba yin irinta ba, ya sa mai girma shugaban kasa Deby ya tada runduna har ya sha alwashin sai ya ga bayan duka ‘yan ta’addan.

Watanni hudu da Chadi ta kai wannan hari, ‘yan ta’addan sun sake kawo mata farmakin da aka kashe sojoji hudu, amma duk da haka, Deby ya ce babu ‘yan ta’addan a kasarsa.

Deby ya ce Boko Haram su na kawo masu hari ne daga bakin iyakokin ta Nijar da Najeriya. Shugaban kasar ya ce ‘yan ta’addan su na yi masu wannan samame ne cikin dare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel