Binciken EFCC: Kwamiti na iya karkare aiki game da Ibrahim Magu kwanan nan

Binciken EFCC: Kwamiti na iya karkare aiki game da Ibrahim Magu kwanan nan

A makon nan da aka shiga ne ake tunanin cewa kwamitin da aka kafa domin ya binciki tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, zai kammala aikinsa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa watakila wannan kwamiti da shugaban kasa ya ba alhakin gudanar da bincike a kan aikin EFCC, ya gabatar da sakamakon aikin da ya yi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba wannan kwamiti na musamman tsawon kwanaki 45 ya karkare binciken zargin da ke kan wuyan tsohon shugaban hukumar EFCC.

A takardar da shugaban kasa ya sa hannu domin bada iznin binciken badakalar da ke kan Ibrahim Magu, ya nemi a duba duk ayyukan da EFCC ta yi tsakanin 2015 zuwa 2020.

A wannan takarda mai suna: ‘Instrument Constituting a Judicial Commission of Inquiry for the Investigation of Mr. Ibrahim Magu, the Ag. Chairman of the EFCC for Alleged Abuse of Office and Mismanagement of Federal Government Recovered Assets and Finances from May 2015 to May 2020’, Buhari ya ba mutane bakwai nauyin wannan aiki.

KU KARANTA: Ana zargin an yi awon gaba da ruwan da aka samu daga kudin EFCC

Binciken EFCC: Kwamiti na iya karkare aiki game da Ibrahim Magu kwanan nan
Ayo Salami ne shugaban kwamitin binciken EFCC
Asali: UGC

‘Yan kwamitin sun hada da Ayo Salami a matsayin shugaba da kuma DIG Michael Ogbezi, Muhammad Babadoko (daga ma’aikatar shari’a) da Hassan Abdullahi (daga DSS).

Sauran ‘yan kwamitin su ne: Muhammad Shamsudeen (OAGF), Douglas Egweme (NFIU), sai kuma Kazeem Atitebi wanda shi ne sakataren kwamitin binciken.

Kwamitin ya kunshi wakilai daga kowane bangare na fadin kasar wanda su ka soma aiki a ranar 3 ga watan Yuli. Ana sa ran su gabatar da rahotonsu kafin ranar 19 ga watan Agustan 2020.

Idan abubuwa sun tafi daidai, a cikin makon nan shugaban kasa zai karbi rahoton aikin da aka yi. Kwamitin ya saurari ta-bakin jama’a, sai dai an yi wannan ne ba a bainar jama’a ba.

Ana binciken Magu da laifuffukan da su ka hada da rashin gaskiya, watsi da umarnin kotu. Sai kuma saida kadarorin da aka karbe daga hannun barayi, da bi ta kan dukiyar gwamnati.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel