Mataimakin gwamnan Edo ya yi zargin cewa wasu manya na shirin kashe shi
- Philip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo ya zargi wasu manyan masu ruwa da tsaki a jihar da shirya munakisa domin kashe shi
- Ya ce sun shirya hakan ne ta hanyar turo wasu mutane jihar domin su aiwatar da mugun nufin kansa da wasu sanannu
- Mataimakin gwamnan ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umurci hukumomin tsaro da su yi aikinsu don hana jihar zama filin yaki
Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya yi zargin cewa wasu manyan masu ruwa da tsaki a jihar na kulla-kulla domin halaka shi.
Mista Shaibu ya fadi hakan ne a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, yayin wani taron manema labarai a birnin Benin, Channels TV ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: An bani goron gayyatar koma wa APC - Ortom
"Mun samu bayanan kwararru cewa wasu mutane na a jihar Edo kuma aikin da aka turo su yi shine su zo su kashe wasu sanannun mutane a jihar.
“Don haka ina sanar da jama’a cewa wadannan mutane na a gari kuma mun kira hukumomin tsaro game da ayyukansu da kuma dalilin da yasa suka shigo garin.”
Shaibu ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umurci hukumomin tsaro da su “yi aikinsu saboda jihar Edo ba zai zama filin yaki ba idan har aka magance wadannan abubuwan.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma a Delta
“A garemu, za mu ci gaba da rokon mutanenmu da kada su nemi rigima.”
Mataimakin gwamnan ya ci gaba da cewa “kada ku tarwatsa kowani taro. Mu masu bin doka ne. Muna da hakki na kare rayuka da dukiyoyi. Za mu ci gaba da yin wannan.”
A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamnonin jam'iyyar APC sun tsinkayi birnin Benin, a jihar Edo a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta.
Sun je jihar ne don kaddamar da yakin neman zaben gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar wanda za a yi a ranar 19 ga watan Satumba a jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://facebook.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng