Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma a Delta

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma a Delta

- ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Warri ta arewa

- An sace shi ne a ranar Asabar da yamma

- Rundunar ‘yan sandan jihar yan tabbatar da lamarin, tace tana kokarin ceto shi

Wasu 'yan bindiga sun sace shugaban karamar hukumar Warri ta Arewa a jihar Delta, Aduge Okorodudu.

An tattaro cewa an sace shugaban karamar hukumar ne a yammacin Asabar a kan babbar hanyar Mbiaku da ke Warri.

'Yan bindigar sun harbi direban shugaban karamar hukumar kafin daga bisani su yi awon gaba da uban gidansa.

KU KARANTA KUMA: Edo 2020: Mun zo sake karbar jiharmu - Mai Mala

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma a Delta
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma a Delta
Asali: UGC

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Garba, yayin tabbatar da aukuwar lamarin ga AIT.live, ya ce 'yan sanda na iyakar bakin kokarinsu wurin bankado inda aka kai shugaban karamar hukumar.

A wani labarin, rundunar ‘yan sanda, ta sanar da cewa ta samu nasarar kashe wasu mutum takwas da ake zargi ‘yan daban daji ne a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Hakan ya fito ne daga bakin babban jami’i mai kula da hulda da al’umma na rundunar ‘yan sandan, Gambo Isah, cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a birnin Dikko.

Ya ce a ranar 6 ga watan Agusta, wata tawagar ‘yan sanda ta kai simame kauyen Zamfarawa na karamar hukumar Batsari, bayan samun rahoton cewa ‘yan daban daji fiye da 40 sun kai hari kauyen da bindigu kirar AK 47.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2023: PDP za ta kwace mulkin Najeriya daga hannun Buhari – Bala Mohammed

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce ‘yan ta’addan sun harbe wani Shafi’i Suleiman mai shekaru 65 da kuma Yakubu Idris mai shekaru 70, baya ga shanu da dama da suka yi awon gaba da su.

A cewarsa, ‘yan ta’addan sun yi wa tawagar jami’an kwanton bauna a kan hanyarsu ta zuwa kauyen, inda suka yi gaggawar mayar da martini da har suka samu nasarar kashe daya daga cikin maharani.

Ya kuma ce da dama sun tsere da raunuka na harbin bindiga kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng