Edo 2020: Mun zo sake karbar jiharmu - Mai Mala

Edo 2020: Mun zo sake karbar jiharmu - Mai Mala

Gwamnonin jam'iyyar APC sun tsinkayi birnin Benin, a jihar Edo a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta.

Sun je jihar ne don kaddamar da yakin neman zaben gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar wanda za a yi a ranar 19 ga watan Satumba a jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

Gwamnonin da suka hallara sun hada da Gwamna jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Dapo Abiodun na jihar Ogun, Gboyega Oyetola na jihar Osun, Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, Abubakar Bello na jihar Neja da Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Sauran sun hada da Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Abubakar Bagudu na jihar Kebbi, Muhammad Badaru na jihar Jigawa, Hope Uzodinma na jihar Imo.

Edo 2020: Mun zo sake karbar jiharmu - Mai Mala
Edo 2020: Mun zo sake karbar jiharmu - Mai Mala Hoto: The Cable
Asali: UGC

Sai kuma Mai Mala Buni na jihar Yobe, wanda shine shugaban rikon kwarya na jam'iyyar.

Sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka hallara sun hada da Ovie Omo-Agege, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Rotimi Amaechi, ministan sufurin da Edward Onoja, mataimakin gwamnan jihar Kogi.

Mala Buni, yayin bayyana Osagie Ize-Iyamu a matsayin dan takarar jam'iyyar, ya sanar da magoya bayan jam'iyyar cewa gwamnonin sun bayyana ne don sake karbe jihar.

"Mun zo jihar Edo ne don karbar kayanmu," Mala Buni yace.

"A shekaru hudu da suka gabata, mun zo nan kuma kun zabi APC kuma mun san za ku sake aikata hakan. Muna kira gareku da kada ku tada hankula saboda nasara tamu ce kuma mun zo samunta ne."

Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar na kasa, ya ce Ize-Iyamu zai kafa gwamnati da za ta taba rayuwar mabukata tare da daga darajarsu.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Tinubu ya fusata da Obaseki – PDP

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa jam'iyyarsu ta Peoples Democratic Party (PDP), za ta lashe zabe a 2023.

A wata hira da gwamnan ya yi da sashin Hausa na BBC, ya ce kawunan yan jam'iyyar APC duk a rarrabe yake, cewa sun hadu ne ta wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari kawai.

Gwamnan ya kuma jadadda cewa akwai kyakyawar alaka tsakaninsu da gwamnonin APC a gwamnatance, sani da kuma fahimtar menene gwamnati.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng