Dalilin da yasa Tinubu ya fusata da Obaseki – PDP
- Kwamitin kamfen din jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Edo na ranar 19 ga watan Satumba, ya bayyana dalilin da ya sa Tinubu ya fusata da Obaseki
- Ya ce Tinubu ya yi fushi da Obaseki ne saboda ya ki zama dan abi yarima a sha kidan APC
- Hakazalika, shugaban kwamitin kamfen din zaben gwamna na PDP a jihar Edo, Cif Dan Orbih, ya shawarci Tinubu da ya bari mutanen Edo su zabi wanda zai shugabance su
Kwamitin kamfen din jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Edo na ranar 19 ga watan Satumba, ya yi zargin cewa shugaban jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, ya fusata da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ne saboda ya ki zama dan abi yarima a sha kidan APC.
Tinubu a daren ranar Juma’a ya bayyana cewa Obaseki ya aikata laifin da ya kamata a tsige shi kan rawar ganin da ya taka a rikicin da ya addabi majalisar dokokin jihar Edo.
Ya bayyana a wani jawabi cewa kewaye majalisa da aka yi domin hana rantsar da kaso biyu cikin uku na ‘yan majalisar dokoki na APC ya kasance ba’a ga kundin tsarin mulki.
Amma a wani jawabi daga sakataren kwamitin kamfen na PDP, Kola Ologbondiyan, a ranar Asabar, ya ce Obaseki ya shiga cikin makiyan Tinubu ne saboda ya ki bari APC ta yi yadda ta ga dama da baitul-malin APC.
Kwamitin kamfen din na PDP ya ce kokawar da Tinubu ke yi ya kara tabbatar da zargin cewa bangaren dokokin Edo na da goyon bayan shugabancin APC don wasu dalilai na su.
Hakazalika, shugaban kwamitin kamfen din zaben gwamna na PDP a jihar Edo, Cif Dan Orbih, ya shawarci Tinubu da ya bari mutanen Edo su zabi wanda zai shugabance su.
KU KARANTA KUMA: Abubuwa 12 da ya kamata ku sani game da marigayi Sanata Buruji Kashamu
“Tinubu ya kyale Gwamna Obaseki saboda shi ba dan iko bane kamar shi,” cewar Orbih a wani jawabi da ya fitar a ranar Asabar.
Ya ce tsarin siyasar Tinubu baya burge mutanen Edo, inda ya kara da cewar, “babu ma’ana da zai zauna daga Lagas yana jero laifukan zababben gwamnan jihar Edo don tsige shi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng